Hukumar Bunkasa Aikin Noma da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA), ta horar da manoman Wake tare da ba su kayan aiki; don kara habaka nomansu.
Manoman da suka amfana da horon, sun bayyana jin dadinsu musamman ta fuskar ba su sabon Irin Wake da aka yi; domin amfanuwarsu.
- Kirismeti: Shugaban Karamar Hukumar Soba Ya Tallafa Wa Kiristoci Da Buhunan Shinkafa Fiye Da 500
- Mutum 2 Sun Mutu Yayin Da ‘Yansanda Suka Ceto Mutum 10 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Katsina
Manajan Darakta na Hukumar ta KNARDA, Dakta Farouk Kurawa ya bayyana cewa, Hukumar tasa a karkashin shirin aikin bunkasa aikin noma da Bankin Musulunci na Bunkasa Aikin na Noma (IsDB), tare da tallafin Shirin Inganta Rayuwar Alumma (LLF) ne suka zuba kudede tare da raba wa manoman sabon Irin na Wake.
Kurawa ya sanar da cewa, an raba wa manoman Irin ne, domin kara habaka noman Wake da kuma bunkasa girbinsa a jihar.
Manajan ya bayyana haka ne, a jawabinsa yayin samar da wannan dauki a kauyen Riga Fada da ke Karamar Hukumar Kumbotso a jihar.
A cewar Kurawan, an samu nasarori da dama a karkashin wannan aiki, inda ya kara da cewa, kamar sauran sassan Nijeriya; su ma manoman da ke Jihar Kano, sun samu bayanai; musamman a kan noman rani.
Shi ma a nasa jawabin, wani jami’i a hukumar ta KNARDA Muhammad Ahmad Nahannu ya bayyana cewa, sabon Irin Waken; na samar da girbi mai yawa fiye da Irin Waken da manoman suka saba shukawa, wanda ya kai kashi goma na rubun da ake samu a girbin.
Ahmad ya kara da cewa, sama da rukunin al’umma 258 da suka hada da mata 25 daga kowanne cikin rukuni, sun amfana da wannan tallafi daban-daban na wannan aiki.
Shi kuwa, Ko’odinetan aikin na KSADP a Jihar Kano, Malam Ibrahim Garba ya bayyana cewa, Gwamnati ce ke taimaka wa aikin, musamman don kara habaka fannin aikin noma ta hanyar bayar da tallafin kayan aikin noma, bayar da rancen noma, sama wa manoma kasuwa da sauran makamantansu.
Daya daga cikin manoman da suka amfana da tallafin, Malam Auwal Isah Kumbotso ya bayyna cewa, bisa wannan ci gaba da aka sama musu a karkashin wannan aiki, nan ba da jimawa ba; Jihar Kano za ta zama cibiyar noman Wake.
Kumbotso ya kara da cewa, bisa wannan mayar da hankali da aka yi, hakan ya nuna cewa, gwamnatin jihar za a kara nuna sha’awa a aikin noma fiye da yadda ake da sha’awarsa a baya.
A cewarsa,“Mun gamsu da sabon Irin Waken da aka raba mana, domin Iri da aka yi gwajinsa, mahukunta sun aminta da shi”.
Ya kara da cewa, daukacin wadanda suka amfana da sabon Irin, mun tabbatar da hakan domin sakamakon da muka samu daga yin amfani da sabon Irin, mun gamsu da haka.
Ya sanar da cewa, a matsayina na manomi; zan iya bayar da shedar cewa, girbin da na yi na sabon Waken sau biyu; ya rubanya girbin da na yi a bara.