Connect with us

LABARAI

Hukumar Kwashe Shara Na Ci Gaba Da Tsaftace Kano

Published

on

Kumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano, a karkashin manajan daraktan hukumar Injiniya Muhammad Adamu Bichi, na bakin kokarinta wajen ganin ta kwashe sharan dake cikin kwaryar birnin Kano musamman wuraren da aka tanada domin zuba shara.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar Malam Muhammad Arabiyu Garba, alokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin hukumar.Muhammad Arabiyu Garba domin ganin Kano ta samu kulawa ta musamman akan tsaftar muhalli ya sa akullum sai suna da jadawalin fita lunguna da sako sako domin kwashe sharan inda ake fita da manyan motocin kwashe shara da ma’aikata .

Sai dai Arabiyu Garba, ya nuna damuwar shi  game da yadda wasu mutanen ke zubar da shara akan hanyoyin da al’umma ke bi ko kuma kan hanya musamman ahanyoyin ruwa na cikin unguwannin dake Kano.

Sai ya yi kira ga al’ummar jihar ta Kano da su rika zubar da shara a wuraren da aka tanadar , matukar aka zubar da shara barkatai ko kuma wuraren da bata kamata ba tana jawo illoli ga lafiyar al’umma kamar zazzabin cizon Sauro tare da gurdatar muhalli da sauran su.

Daga karshe ya godewa wasu al’ummar game da yadda suke sanar da su domin zuwa a kwashe sharan dake cikin unguwannin su ko kuma wuraren da aka tanada domin zuba shara. pid manajan daraktan kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Injiniya Muhammad Adamu Bichi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: