Hukumar hana fasa kwabri ta kasa reshen jihar Katsina ta yi nasarar kama kayan maye da motoci guda biyu wanda kudin ya kai naira miliyan 721,592,250 a Katsina.
Wannan nasara dai sun same ta a yankin Daura akan iyakar Nijeriya da kasar Nijar inda ake kokarin shigowa da wadannan haramtattu kayayyaki.
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Xi Jinping Ya Halarci Bikin Cika Shekaru 60 Da Kafuwar Jihar Xizang Mai Cin Gashin Kanta
Da yake jawabi a lokacin taron manema labarai a Katsina shugaban hukumar Idris Abba Aji ya bayyana wannan nasara a matsayin ta kasa baki daya.
Ya kara da cewa irin wadannan kayayyakin maye ne ake kaiwa ‘yan ta’adda domin su ci gaba da kai wa al’umma hare-haren wuce gona da iri a jihar Katsina da arewacin Nijeriya baki daya.
Abba Aji wanda ya ce kama wadannan kayayyaki za su taimaka wa kokarin jami’an tsaro da gwamnati wajen ganin an kawo karshen matsalar tsaro a Nijeriya musamman yankin arewa da batun ya fi kamari.
Shugaban hukumar hana fasa kwabri ta kasa ya ce sun kama kwali goma sha hudu na Tramadol wanda kudin da ya kai naira miliyan 650 da kuma pregabalin kwali 38 wanda kudin da ya kai naira miliyan 28,500
Kazalika ya ci gaba bayanin cewa sun kama tabar wiwi wanda ya kai kulli 174 kudin ta sun kai naira miliyan 1,807,250 .
“Duk a lokacin wannan kamen mun samu nasarar kama motoci guda biyu Toyota land cruiser mai launi ash mai lamba ABJ 451 AP Abuja wanda kudin ta suka kai miliyan 10,509
Sai kuma Toyota Jeep land cruiser baka mai lamba YAB 935 BJ Abuja wanda suka ce kudin ta zai kai naira miliyan 12,600.
A cewar sa, sun kama wadannan motoci bisa bayanan sirri da suka samu wanda kuma sun cafke mutum guda wanda yanzu an ba da belin sa kafin ranar zuwa kotu.
Ya kara da cewa jama’a sun fara korafi a kan yadda jami’an tsaro na Kwastam ke tare manyan motoci a kan hanya wanda ya ce labarin sirri da suke samu ya sa suke yin haka wanda yanzu ga nasara an samu.
“Yanzu an fito da sabbin dabarun yin fasa kwabri inda ake amfani da manyan motoci Na alfarma wanda ake sa ran cewa ba za a iya tsaida su a kan hanya ba, sai a dauko kayan laifi a wuce da su,”inji shi
Idris Abba Aji ya ce jami’an da da sauran jami’an tsaro a shirye suke wajen ganin sun taimaka wa kokarin da gwamnati ke yi na dakile shigowa da muggan kwayoyi domin kaiwa ‘yan bindiga.
Kazalika ya nuna irin illar da shigowa da irin wadannan kwayoyi ke yi wajen ba da aiki baya musamman fada da ‘yan bindiga da mafi yawan su sai shi. Sha kwaya kafin su kai hare-haren wuce gona da iri.
Daga karshe ya yi fatan cewa al’umma su ci gaba da taimaka masu da bayanan sirri domin ganin an samu nasarar da ake bukata a Nijeriya da kuma jihar Katsina.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp