Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (Kwastam), ta nada Abdullahi Aliyu Maiwada a matsayin sabon mai magana da yawun hukumar.
Shugaban hukunar Kanal Hameed Ibrahim Ali mai ritaya ya bada umarnin nada CSC Maiwada bayan duba nagarta da kuma iya aikinsa shekara da shekaru a hukumar.
- Burundi Na Yabawa Tallafin Kasar Sin A Fannin Raya Noma
- ‘Yan Daba Sun Kai Wa Dan Takarar Gwamnan APC A Ribas Hari
Maiwada dai ya taba zama kakakin hukumar na Shiyya ta biyu ta hukumar kwastam dake Kaduna ya kuma rike wannan mukami a jihar Ogun dake arewa maso yamma na tsawon shekaru.
Ya dawo shalkwatar hukumar a shekarar 2020 inda ya zama jami’in hulda dake tsakanin gidan jarida na Kwastam da jami’an kwastam a bangarorin Nijeriya.
Maiwada yayi digirinsa na farko a jami’ar Bayero a yanzu yana da digiri na biyu guda biyu kuma yana digiri na uku a harkar jarida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp