An bukaci alummar Musulmi a kasar nan, da su yi watsi da batun cewa, amfani da kayan gona da aka samar ta hanyar sanadarin fasahar halittu, zai iya shafar lafiyarsu kuma hakan, ya sabawa addininsu.
Shugaban Hukumar Bunkasa Kimiyyar Fasahar Bazarin Halittu ta kasa ta NABDA Farfesa Abdullahi Mustapha, ya yi wannan kiran a taron wayar da kan alummar Musulm a Abuja kan batun yin amfani da sanadarin fasahar halittu.
- Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure
- CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD
“Mun sane da cewa, addininmu na Musulunci, ya koyar da mu cin abinda yake halal da kuma hana mu cin abinda yake haram,”Inji Mustapha.
“Nauyi a kanmu mu tabbatar da cewa, mu bi ka’idojin Shari’ar Musulunci wajen yin amfani da duk wani na’uin amfanin gona da zai iya shafar kiwon lafiayarnu ko kuma su zubar mana da mutuncinmu,” A cawar Shugaban.
Taron ya samu halartar kwararru a fannin Kimiyyar Fasahar Zamani da Shugabanin Hukumomin da ke sanya ido a bangaren amfanin gona inda suka gabatar da jawabai kan batun yin amfani da sanadarin fasahar halittu da kuma kare lafiyarsu.
Bugu da kari, Mustapha ya buga misali da amfanin gona da ake shukawa masu jure yanayin Fari wadanda kuma ke dauke da sanadarin bitamin da sauran nau’un kimiya.
“An samar da su ne, domin a bunka samar da amfanin gona mai yawa da habaka kayan gona masu dauke da sanadarin gina jiki da kuma dakile yin nasarar amfanin gona kafin yin girbi,mussaman saboda marsalar sauyin yanayi,” A cawar Mustapha.
Shi ma a na sa jawabin a wajen taron kwarare a bangaren renon Irin Farin Wake na sanadarin fasahar halittu Farfesa Mohammad Faguji Ishiyaku ya shedawa mahalarta taron cewa, ko kusa ba zai taba shiga cikin fannin ba idan har shugarsa, za ta, cutar da Musulmin kasar nan ba.
Mohammad wanda ya fito daga Jamai’ar Ahmadu Bello da ke garin Zaria, ya shedawa mahalrta taron cewa, abinda ake yadawa kan batun na irin wadannan amfanin gonar kitsawa ne kawai da wash ‘yan kasuwa a fannin suka yi wanda kuma ba su da wata kwakwarar sheda ta bayanai ,kan ikirarin na su.
Ita kuwa a na ta jawabin tun da farfko a wajen taron Darakta s Hukumar ta NABDA Dakta Rose Madwell Gidado ta bayyana cewa, “Amfanin gonar na sanadarin fasahar halittu na ragewa manoma dogaro kan kayan feshi da kuma kare lafiyarsu daga kamuwa da illolin da magungunan feshen, za su janyo masu,” Inji ta.
“Masu bincike sun tabbatar da cewa, amfanin gonar da aka shuka ta hanyar Fasahar jinsin fasahar halittu na rage yawan nome Ciyawa a gonakai da rage yawan yin amfani da magungunan feshi da rage zaizayar kasa da kuma bai wa kasar noma kariya, ” A cawar Daraktar.
Shi kuwa Jami’in gudanarwa da shirye-shirye a Gidauniyar Kimiyyar Aikin Noma ta Afirka AATF Dakta Ehirim Bernard ya yi nuni da cewa, sanadarin proteins na sabon Farin Wake, na da dogon tarihi wanda ya faro tun a shekarar 1950 kuma ba tare da haifar da wata illa ga lafiyarsu mutane ba.
Ya kara da cewa, haka kuma ana yin amfani da na Masara tun a shekarar 1996 kuma bata taba yin wata illa ga lafiyar mutane ba.
Ya yi nuni da cewa, an shafe shekaru ana yin amfani da nasarar da aka shuka mai jurewa ko wanne Irin yanayi na fari kuma ake kaita kasuwanni domin siyarwa kuma ba a taba samun wani rahoton ko ta cutar da wani ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp