Hukumomi 428 Ba Za Su Iya Biyan Albashin Nuwamba Ba – Gwamnatin Tarayya

Kwarewa

Daga Mahdi M. Muhammad

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, kimanin hukumomi 428 ba za su iya biyan albashi a karshen watan Nuwamba ba. Shugaban ofishin Kasafin Kudi, Ben Akabueze, ne ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati.

Ya kara da cewa, hakan zai kasance ne a sanadiyyar shirya kasafin kudin shekarar 2019 kafin gwamnatin tarayya ta sanar da sabon tsarin mafi karancin albashi.

kabueze, ya ce, gwamnati na nazarin sakin kudade daga cikin sabbin tsari domin biyan gibin da ke cikin albashin ma’aikata na watan Nuwamba. Kimanin hukumomi 428 ba za su iya biyan albashi a karshen watan Nuwamba ba. Watakila za mu bukaci dauka daga cikin wididdigar sabis don kula da dan gajeren faduwar albashin ma’aikata,” in ji shi.

A halin da a ke ciki yanzu, shugaban kwamitin, Sanata Mathew Urhoghide, ya zargi zartarwa da gangan a karkashin bayar da kudi ga Ofishin Odita-Janar na tarayya.

Ya kuma nuna mamakinsa kan yadda wata hukuma wacce aka kafa don yaki da cin hanci da rashawa a makarantu ba ta samun isassun kudade daga bangaren zartarwa, yayin da sauran hukumomin kamar hukumar yaki da cin hanci da tattalin arzikin kasa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa masu zaman kansu suke samun kudaden da suka dace.

Da ya ke mayar da martani, Akabueze ya ce, ofishin kasafin kudin zai dace ne kawai da kudin da ya dace ga ofishin Odita janar na tarayya bisa dogaro da dokokin da ke akwai.

 

Exit mobile version