CRI Hausa" />

IMF Ya Yi Hasashen Farfadowar Tattalin Arzikin Sin A Rubu’i Na biyu Na Nana

Manajar daraktar gudanarwar asusun bada lamini na duniya (IMF), Kristalina Georgieva ta sanar a jiya Asabar cewa tana tsammanin tattalin arzikin kasar Sin zai iya komawa daidai a rubu’i na biyu na wannan shekara ta 2020.
Georgieva ta ce, ta yi kyakkyawar tattaunawa da jami’an kasar Sin, a cewarta, huhumomin kasar Sin suna aiki tukuru wajen daukar matakan rage illolin da cutar numfashi ta COVID-19 za ta iya haifarwa ga tattalin arzikin kasar.
Ta ce, bisa ga irin tanade-tanaden da aka yi idan an kammala aiwatar da su tattalin arzikin kasar Sin zai iya daidaituwa a rubu’i na biyu na bana.
Georgieva ta fada a lokacin taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kasashen G20 cewa, a bisa wannan sakamako, tasirin da matsalar za ta yi ga tattalin arzikin duniya ba ta da girma sosai kuma na gajeren lokaci ne.
Sannan, babban direktan sashen jarin waje na ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Zong Changqing ya bayyana a kwanan baya cewa, cutar numfashi ta COVID-19 ba za ta illata kasar Sin na dogon lokaci ba, hakan ya sa, karfin da Sin take da shi na jawo jarin waje bai canja ba, imani da kuma tsarin da yawancin kamfanonin ketare ke da su dangane da zuba jari a kasar Sin ba su canja ba.
An kiyasta cewa, Sin za ta dauki matakan da suka dace don habaka sana’o’i da za su shigo da jarin waje, don kara kyautata yanayin zuba jari a kasar. (Masu Fassarawa: Ahmad Fagam, Amina Xu)

Exit mobile version