Mustapha Abdullahi" />

In Dai PDP Na Son Samun Nasara, To Ta Sa Mata A Gaba – Amina Soba

Magance Matsalar Tsaro

Hajiya Amina Adamu Soba, Tsohuwar ‘yar takara ce a jam’iyyar PDP a neman kujerar Majalisar wakilai ta tarayya, ta bayyana cewa matsalar fahimtar Juna ce kawai ke cikin jam’iyyar PDP, amma ba sabani ko rabe-rabe, kamar yadda wasu ke kokarin nunawa ba.

Ta ce, hadin kai a zauna a yi shirin zaune da ya fi na tsaye a sasanta a dukkan al’amura ne ta yadda kowa zai fahimci dan uwansa ne ya kamata.

Ta ce, “duk bangaren da ake cewa sun rike komai, a sasanta, su saki wadansu abubuwa domin a cimma nasara a damben naushin da ake bukatar a yi a nan gaba kadan.

Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke ganawa da manema labarai a ofishin PDP na Jihar Kaduna da ke NDA.

In da ta ci gaba da cewa, ta yaya ana korafin cewa wani bangare ya kama komai ya rike, sannan wasu da ake zargi da haka za su yi shiru su kasa daukar mataki, duk da sanin irin babban aikin da ke gaban ‘ya’yan Jam’iyyar PDP da kasa baki daya domin ganin mulki ya dawo hannun jam’iyyar da za ta taimaki ‘yan Nijeriya, wato PDP.

Hajiya Amina Adamu Soba, ta kuma yi bayani a game da irin tasirin mata a lamarin zabe da kuma harkokin siyasa baki daya, inda ta yi kira ga jam’iyyar PDP a kowane irin mataki, tun daga sama har kasa da a tabbatar da an jawo mata, sakamakon irin tasirin da suke da shi a lokacin zabe.

“Hakika mata su ne ke yin zabe kuma su ne siyasar, har ma mulkin baki daya, domin duk Namijin da bai samu komai ba game da nagartar mace a cikin gida ba zai iya gudanar da komai ba a rayuwa, ko da kuwa ya je zaman ofis, ba wani abin da zai gudana. Saboda haka mata ba abin a bar su a baya ba ne ga duk mai hankali, in ji ta.

Ta kara da cewa, “duk inda aka sanya maza uku, to a nemo  mace ta zama ta hudu, in kuma an sa maza hudu, to a nemo mata biyu su zama su shida domin a samu tafiyar da aiki kamar yadda ya dace. Mata da ake gani, Allah ya ba su basirar hakuri, juriya da hangen nesa, saboda mace mai juriya da tunani za ta iya ba Namiji shawarar da shi ba nan ya hango ba, kuma idan ya yi aiki da abin, zai ga ai nan ne nasarar ta ke. Wannan ne nake son jam’iyyar PDP ta gane a dukkan shawarwarinta da rufe kofar da za ta yi ta tabbatar akwai mata a dukkan al’amuranta baki daya in ana son cimma nasara.

Exit mobile version