Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa yana da cikakkiyar kwarewar shugabancin majalisa fiye da shugaban majalisar da ke kai, Sanata Akpabio.
Ndume ya bayyana hakan ne a lokacin wata hira da jidan talabijin na Channels.
- Zamu Sabanta Dakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita
- Baje Kolin CIIE Na Kara Jan Hankalin Sassa Kasa Da Kasa
Da yake magana a kan irin tsarin salon Akpabio a matsayin shugabancin majalisar dattawa ta 10, Ndume ya ce, ““Matsalata ita ce yadda ya tafiyar da lamarin, kuma abin da ya faru na karshe shi ne, an samu rashin fahimta ko kuma an sauka daga kan layin abin da ake tattaunawa a kai. Kar ku manta ana na yi yaki da kuma gwagwarmaya kan ganin an zabi Akpabio. Mutum ba zai iya gina gida kuma lalata da hannunsa.
“Babbar matsalar a nan ita ce, ina da kwarewa shiye da shi. a duk lokacin da na yi kokarin yi masa kyara, sai ya ce zan tsallaki iyakata na matsayin mai tsawatarwa na majalisar dattawa, ya kamata in kasance wanda zai iya maido da shi kan layi a duk lokacin da ya saba layi.
“A wancen lokaci, ya kamata ya gayyace ni sai mu kara tattaunawa kan maganar daya bayan daya, amma ya yi amfani da kujeransa, wanda kuma ya kasance a daidai karfe 12:30 na rana, lokacin kuma ina bukatar in je in yi sallah.”
Idan za a iya tunawa dai, Ndume ya fice daga zauren majalisar dattawa bayan takaddama da ta barke tsakaninsa da Akpabio a ranar 19 ga watan Oktoban wannan shekara.