Abba Ibrahim Wada" />

Ina Goyon Bayan Arteta Kan Wariyar Launin Fata – Guardiola

Guardiola

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa, yana goyon bayan kalaman da kociyan Arsenal Mikel Arteta yayi akan cewa yakamata a kawo karshen wariyar launin fatar da ake nunawa ‘yan kwallo da masu koyarwa da kuma alkalan wasa.

Ranar Juma’a ne mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bi sahun masu horarwa wajen kiraye-kirayen daukar mataki kan kafofin sada zumunta da nufin kawo karshen cin zarafi ko kuma nuna wariyar da ‘yan wasa ke fuskanta, kiran da ke zuwa bayan Kocin ya fuskanci barazana kan iyalansa a baya-bayan nan.
Arteta dan asalin kasar Sipaniya ya ce yanzu haka amfani da shafinsa na Twitter ya gagareshi saboda fargabar barazanar da ake masa, inda ya ce wajibi ne kamfanonin da ke kula da shafukan su dauki matakan gaggawa la’akari da yadda hakan ke shafar harkokin wasanni a Ingila.
Ko a baya-bayan nan sai da hukumar wasanni ta Birtaniya ta aikewa da kamfanonin sada zumuntar bukatar daukar tsauraran mataki kan masu amfani da fagen wajen nuna wariya, batanci ko kuma barazanar cin zarafi kan ‘yan wasa da masu horarwa har ma da alkalan wasa.
‘Yan wasa irinsu Marcus Rashford na Manchester United da Adel Tuanzebe baya ga Anthony Martial da kuma Lauren James ta tawagar mata da Romaine Sawyers da kuma Reece James na Chelsea, na cikin wadanda suka fuskanci kalaman wariya ta shafukan Intanet a baya-bayan nan.
A bangare guda mai horar da kungiyar Newcastle Stebe Bruce ya ce ko a makwan nan sai da ya fuskanci kalaman barazana tare da yi masa fatan mutuwa, ya yinda alkalin wasa Mike Dean ya janye daga alkalanci a wasannin jiya da yau bayan barazanar kisan da ya fuskanta daga magoya bayan kwallo a Ingila.
Daman dai masu horarwa suna ta kira ga hukumomin da abin ya shafa akan su dauki mataki akan wanda duk aka kama yana nuna wariyar jinsi ko kuma barazana ga lafiya ko kuma rayuwar wani dan wasa mai koyarwa ko kuma alkalin wasa domin tsaftace harkar.

Exit mobile version