Mace ta ba da jikinta ga mata ‘yan’uwanta don a yi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramun ne?
Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta?
In haramun ne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata ‘yar’uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaa.
To ‘yar’uwa malamai sun yi sabani game da tsaraicin mace ga ‘yar’uwarta musulma, akwai wadanda suka tafi a kan cewa: bai halatta ‘yar’uwarta mace ta ga
wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune i-su-i-su, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka.
Sai dai abin da mafi yawan malaman fikhu suka tafi a kai shi ne: al’aurar mace ga.
‘Yar’uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa, kamar yadda al’aurar maza take a tsakaninsu.
Don haka bai halatta ta bari wata mace ta kalli sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za a je dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido .
Sannan a bisa wannan bayanin da kika yi, dilkar da kika siffanta za ta zama ba ta halatta ba, tun da za a ga abin da shari’a ba ta halatta a gani ba.
Allah ne mafi sani.