Babban Malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya ce Nijeriya na fama da “cututtuka” a karkashin gwamnatin jam’iyyar APC, inda ya ce yana tausayin wanda zai zama shugaban kasa a 2023.
Malamin ya bayyana cewa Nijeriya na fama da cututtuka da suka hada da kuturta da ciwon suga da kuma cutar mai karya garkuwar jiki.
- An Harbe Dogarin Mataimakin Sufeton ‘Yansanda Yayin Wani Harin ‘Yan Bindiga A Kaduna
- Yadda Aka Ƙaddamar Da Ƙungiyar SURE 4U Domin Jin Ƙan Marasa Galihu
A kan haka, ya ce shugaban kasa mai jiran gado yana bukatar ya kasance mai hankali da goyon bayan mutane ba dan jeka na yi ka ba.
“Dole ne ya dauki mataki cikin gaggawa kuma dole ne ya sanya himma da maida hankali. Na san yawancin matsalolinmu sun samo asali ne daga muradun kasashen waje, amma duk da haka dole ne a magance matsalolin cikin gida.
“Tattalin arzikin yana cikin mawuyacin hali wanda ke bukatar dan kishin kasa na gaske wanda zai kaddamar da mataka ko da sun kasance masu adawa da waɗannan ƙungiyoyin kamfanoni na ‘karya’ waɗanda ke “Draculas” suna tsotse jini daga cikin al’umma. Ba irin matakan da suka dace cikin gaggawa.”
Fadar shugaban kasa da ke wakiltar mutane a matsayin gangar jiki ba ta san wani irin hali kasar nan ke ciki ba, a cewar shehun malamin.
Ya kuma kara da cewa, shirin da bin diddigi na BBC da na Aminiya suka buga a baya-bayan nan game da tashe-tashen hankula a jihar Zamfara, sun fallasa yadda ainahin rigingimun da yankin Arewa maso Yamma ke ciki.
Ya kawar da cewa dukkan bangarorin biyu ne suka aikata laifukan amma abin bakin ciki shi ne, kasashen waje suna kallon bangare daya a matsayin mai laifi daya tilo, sai dai ya ce gwamnati na kokarin daukar matakin da bai dace ba.