Mohammed Bala Garba" />

Inganta Harkar Ilimi A Kano Ne Mafita Ba Biya Wa Dalibai Kudin Jarrabawa Ba

Najeriya kasa ce dake da mabiya addinai daban – daban, manya a cikinsu su ne addinin Musulunci da Kiristiyaniti, wadanda suka shigo kasar shekaru aru-aru kafin zuwan turawan mulkin mallaka.

Tun daga wannan lokaci ake samun hanyoyin ilimantar da al’umma. Alal misali, a karni na 14, lokacin da Musulunci ya shigo Arewacin Najeriya, aka fara koyar da jama’a harshen larabci ta yadda zasu iya karatun Al-kur’ani mai girma tare da karin ilimi game da addinin.

Ilimin Boko (Ilimin zamani) kuwa, yazo mana Najeriya ta hanyar kungiyoyin mishan a tsakanin shekarar 1842 zuwa 1914, yayin da a tsakanin wadannan shekarun kimanin kungiyoyin mishan-mishan 10 ne suka shigo kasar suna ayyuka daban – daban wadanda suka hada da ilmantar da jama’a wanda suka fi baiwa karfi sosai.

Tun daga wannan lokacin aka fara giggina makarantu ana daukar jama’a musamman yara domin basu ilimi.

A shekarar 1934 a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero, aka fara gina makarantar koyan harshen larabci a Kano, inda ake koyar da shari’ar Musulunci. Bayan wannan kuma ana koyar da Turanci da Lissafi.

Makarantar ta bunkasa sosai, inda cikin kankanin lokaci aka mai da ita ta zama Kwalejin Bayero, wadda ta zama wani bangare na jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, daga bisani kuma ta zama jami’ar Bayero.

Babban matakin yakar talauci dai shi ne ilimi da tarbiya ta gari. To amma duk da wannan buri da aka sa a gaba har yanzu ba ta canza zani ba.

A yau tsarin ilimi a Najeriya ya zama abin da yazama, domin gwamnati kan bar farilai ta kinkimi sunnoni. Kamar yadda a yanzu abin da daliban jihar Kano suke bukata shi ne gwamnatin jihar ta inganta musu harkar ilimi, koda bazata biya musu kudin jarrabawa ba. Idan harkar ilimi ta inganta dalibai suka sami ilimi yadda ya dace! Koda gwamnati bata biya musu kudin jarrabawar ba iyayyensu zasu biya musu.

Amma idan harkar ilimin a gurbace yake, koda gwamnatin ta biyawa dalibai kudin jarrabawa faduwa zasuyi, domin basu da ingantaccen ilimin da zasu ci jarrabawar da shi, inyi-ba-ayi ba kenan.

Kamata ya yi ace gwamnatin jihar Kano ta habbaka harkar ilimi fiye dana baya, tsafanin yadda harkar ilimin ya gurbace akan na bayan. Alai misali, a baya gwamnatin jihar Kano tana dafawa dalibai abinci a makaranta, wanda wannan ya rage makarar dalibai wajen zuwa makaranta, sannan tana dika musu tufafin makaranta kyau, ga litattafai da take basu, ga uwa uba kudin jarrabawar da take biya musu, sannan kuma tana kulawa da malamai iya gwargwado, tsafanin yanzu.

An wayi gari a yau, bawai gwamnatin ta habbaka harkar ilimin ba ma, amfani take da daliban wajen gurbata ilimin. Alai misali, a ranar Alhamis Ashirin da Biyar 25 ga watan Oktoban dubu Biyu da Goma sha Takwas 2018 Miladiyya, gwamnatin jihar tayi amfani da dalibai wajen fito dasu cikin zafi rana daga makarantunsu izuwa sakateriyar gwamnati ta Audu Bako, dauke da takardu an yi rubutu cikin harshen Hausa da Turanci kamar haka:

“Mu bamu yarda ba, sharri aka yiwa Ganduje.”

“Allah ka sakawa mai sharri.”

“We stand with Ganduje.”

“Kano is APC, APC is Ganduje.”

“Jafar, your bideos will not stop us from boting Ganduje.”

“Kano municipal students support 4 + 4.”

“Gyadi Gyadi S .P. S, Jafar Jafar is a great liar.”

“Bamu yarda da bidiyon din Ganduje ba.”  Da dai sauransu.

Shin yanzu wannan habbaka harkar ilimin ne ko gurbata shi? Tsakani da Allah mai ya hada dalibai da wannan harkar?

Daliban da ya kamata a ce suna daukan darasi a cikin ajujuwansu amma gwamnati tayi amfani dasu wajan cin zarafi da tallar karya da gurbata musu tarbiyar ta hanyar tilastarsu daga takardun da baza ma su iya fahimtar wani sako suke dauke shi ba.

Ya kamata gwamnati ta san cewa ‘ya’ya nan iyayyensu amana suka damka mata su don ganin suyi ilimi su zama magina kasa. Kowa na da masaniya akan halin da kasar mu take ciki na hare-haren kungiyar Boko Haram, ba fata nake ba, da ace lokacin da aka fito da wadannan daliban wani abu makamanci haka ya faru da su mai gwamnati zata ce ga iyayyensu?

Bayan haka, dukkan daliban nan ‘ya’yan talakawa ne babu ‘ya’yan masu kudi a ciki, idan hakan kishin Kano da Kanawa ne mai zai hana gwamnati ta sirka da ‘ya’yan manyan jihar Kanon? Ko su basa kishin Kanon ne?

Ta yaya daliban da basu wuce shekaru goma zuwa sha biyar ba, za a sakasu su karyata mutumin da ya ma haife musu da cewa is great liar. Shin wannan habbaka harkar ilimi ne ko gurbata harkar ilimi ne?

Duk wata al’ummar da ke son ci gaba a yau dole ta bayar da cikakkiyar kulawa ga matasanta, tare da basu kyakkyawar horon da ya dace dasu don su zame mata wakilai na gari a duk inda suke.

Sai dai kash! Matasan kasa ta sun zama kashin baya ta bangaren ci gaban al’ummar su, ba tare da la’akari da muhimmancinsu a cikin al’umma ba, da kuma sanin rawar da zasu iya takawa ta fannin gina kasa.

Matasa wakilai ne na samar da zaman lafiya ba hargitsi ba. Domin komai na iya faruwa a duk lokacin da aka tauye musu hakkinsu, ko aka ci gaba da nuna halin ko inkula dangane da rayuwarsu, musamman ma idan babu cikakken tsaro da ilimi da uwa-uba aikin yi, da sauran ababan more rayuwa, wanda ya zama hakki ne na hukuma ta samar dasu. Rashin wadannan abubuwa zai iya jefa su a tsaka mai wuya kamar sace-sace, da yawon banza da sauran aikin ash-sha, wanda kuma bana fatan hakan ta faru gare su.

A kullum al’ummar Najeriya addu’a suke akan halin da kasar ta tsinci kanta, musamman na hare-haren ‘yan tada kayar baya, ga kuma harkar shaye-shaye da tazama ruwan dare ga matasa da ‘yan mata, ga ‘yan fashi da makami, ga masu garkuwa da mutane, ga uwa uba harkar Dabanci da take neman addabar Arewancin kasar. ‘Yan daliban da al’umma ke ganin suna sanyaya musu zuciya wanda suke ganin zasu share musu hawaye nan gaba amma gwamnati na neman gurbata musu rayuwa.

Fatana Allah ya ganar da gwamnatin jihar Kano ta habbaka harkar ilimi a jihar don ganin an samu magina kasa gobe, musamman matasanmu su himmatu wajen neman ilimin addini da na zamani don goben mu ta yi kyawu. Allah ya yi ma na muwakafa.

Mohammed Bala Garba dan Maiduguri ne, mai alfaheri da mahaifar iyayensa, Kanon Dabo. Za a iya tuntubar sa ta wannan lamba 08098331260.

Exit mobile version