Connect with us

WASANNI

Inter Millan Ta Tabbatar Da Neman Ozil

Published

on

Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan, Erick Thohir ya bayyana cewa kungiyarsa tana da niyyar tuntubar dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mesut Ozil dan kasar jamus a watan janairu mai zuwa.

Ozil, wanda ya kara kwantaragin shekaru uku zai iya tattaunawa da kungiyar da take son daukarsa a watan janairu mai zuwa kamar yadda doka tabashi dama.

Tun bayan da kungiyar ta sake sabon mai koyarwa aka fara samun takun saka tsakanin kociyan kungiyar, Unai Emery da Ozil din sakamakon abinda kociyan yace Ozil baya yin wasa da karfinsa.

Shugaban gudanarwar kungiyar yace duk da cewa ba kasafai ake siyan ‘yan wasa a watan janairu ba amma yana tunanin zasu gwada neman dan wasan wanda yayi ritaya daga bugawa kasarsa ta Jamus wasa.

Yace, basu da sa’ar siyan ‘yan wasa a watan janairu domin sun siyo ‘yan wasa irinsu Shakiri da Podolski duk a watan janairu kuma basuyi abin azo agani ba.

Kungiyar Manchester united ma dai ance tana zawarcin dan wasan mai shekaru 29 a duniya wanda yana daya daga cikin ‘yan wasan da suke kokari a kungiyar kawo yanzu

 

Advertisement

labarai