Daga El-Mansur Abubakar, Gombe
Tsohon Kwamishinan ’yan sandan jihar Gombe mai barin gado, Mista Austin I. Iwar, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar hukumar ’yan sandan Jihar a jiya Litinin, yayin da yake mika ragamar mulki ga Sabon Kwamishinan ’yan sandan da aka turo, ya canje shi a aiki, Mista Shina Tahiru Olokulu.
Tsohon Kwamishina Austin Iwar, ya ce jajircewar tasu ce tasa aika-aika ya ragu da kashi 20% cikin 100% a Jihar Gombe, wanda idan aka kwatanta daga watan Janairu na shekarar 2017 zuwa Augustan 2017, da kuma daga Janairu zuwa Agusta 2015.
Ya ce, a tsakanin watanin Janairu zuwa Agustan shekarar 2015 sun samu rahoton fashi da makami guda 45, daga Janairu zuwa Agusta 2017 kuma rahoto 37 aka samu na Luwadi. Inda daga watan Janairu zuwa Agustan 2015 an samu guda 12. A shekarar 2017 kuma an samu guda 7 kacal.
Sauran laifuffukan irin ‘yan bangar siyasa da makamantansu a tsakanin watanin Janairu zuwa Augusta na 2015 suna da rahotanni 10; a tsakanin watanin Janairu zuwa Augusta na 2017 kuma ba a samu ko daya ba.
Kwamishinan ’yan sanda mai barin gado, Austin Iwar, ya ce sauran laifuffuka kuma a tsakanin watanin Janairu zuwa Augusta 2015 suna da rahotannin 884, a tsakanin watanin Janairu zuwa Augustan 2017 guda 729 kawai aka samu.
Daga nan sai Yace a shekara 2 da ya yi a matsayin kwamishinan ’yan sanda a Jihar daga 9 ga watan Satumbar 2015 zuwa 18 ga watan Satumbar 2017 ya samarwa da Matasa ’Yan Kalare ayyukan yi; ma’ana sana’o’in hannu da yawa ta hanyar koya musu sana’o’I, sannanya mayar da sama da dubu 1,500 Makarantar Boko, a shirin ‘Back To Schools Programmes’.