Jakar Magori: Richard Ƙalbul Asad: Mai Zuciyar Zaki (3)

Tare da Nasir Chiromawa 07030863933 (Tes kawai)

Hankalin rundunar Musulmi ya yi matuƙar tashi domin sun fahimci cewa baya ta haihu, labarin da ya riskesu cewa rundunar Jihadin Kirista (Crus) na daf da kar ɓ e iko da Misira babbar Cibiyar Mulkin Daular Ayuby, birnin da Musulmin suka ɗauka a matsayin zuciyar Musulunci ba ƙaramin tayar musu da hankali ya yi ba.

Manyan Kwamandojin Rundunar Musulmai sun bayar da shawarar janyewa daga fagen dagar, domin komawa da baya da nufin kare Misira daga faɗawa hannun Kiristoci.Wannan shawara bata samu kar ɓ uwa a wajen Salahuddin ba, domin ya bayyana musu cewa Mallakar birnin Ƙudus ya fi Misira muhimmanci a wajensa.

Babbar rundunar Kiristoci da ta nufi Misira tana ƙarƙashin babban Kumanda nan Raynaid na Chatillon, shine ya jagoranci rundunar ya durfafi Misra da mayaƙa masu tarin yawa. An tsara cewa bayan kar ɓ e iko da Misira, sai kuma ya haura ta ga ɓ ar ruwan Maliya ya nufi Makka da Madina.

Idan har Raynaid na Chatillon yayi nasarar murƙushe haramin Makka da na Madina, daga nan sai ya juyo da rundunarsa ya biyo biyo ta cikin sahara ya tunkari Salahuddin da rundunarsa, ta yadda za ayi masa ƙofar rago, kafin ya cimma birnin Ƙudus.

A can daya  ɓ an garen kuma Sarkin Ingila Richard da tasa tawagar sunyi shan bante sun challaka ga ɓ ar ruwa sun nufi haryar da zata kaisu birnin Ƙudus. Dubun dubatar Jarumai cike da shauƙi suna faman haɗuwa da rundunar Musulmai domin su ɗanɗana musu azaba.

Rudunar da take gaba wacce take ɗauke da tutoci da kuma wani ƙaton Gicciye (Cross) zaratan Jarumai ne, ‘yan takife, wasu daga cikinsu an ɗauko hayarsu ne da sassa daban daban na Turai, kuma tuni Paparoma yayi musu albishir da Aljanna.

Salahudin ya za ɓ i mutane 500 biyar aga cikin rundunarsa ya umarce su da koma domin su kare Misira daga farmakin Kiristoci, da farko wasu daga cikin Kwamandojinsa sun nuna shakku akan yadda rundunar mutum ɗari biyar zata iya tunkarar gagarumar rundunar da Raynaid na Chatillon ke jagoranta.

Amma daga bisani Salahuddin ya ƙarfafi zuƙatansu inda ya bayyana musu cewa Musulmi ɗaya mai taƙawa kan iya tunkarar mutum goma. Don haka ba tare da  ɓ ata lokaci ba wannan runduna ta mutum 500 biyar tayi harama, suka nufi Misira ta ga ɓ ar ruwa.

Lokaci da suka isa tuni Rundunar Raynald ta kusa cimma Misira, anane aka gwabza mummunan faɗan da Kiristoci suka sha mamaki, ta yadda duk da irin yawan da suke dashi da kuma makaman da suka mallaka, sai da Musulmai suka danna su baya, suka ruguza musu shiri.

Daga yanki kudu da Sahara, an samu ɗauki daga Sarakunan Buzaye, waɗanda suka kawowa rundunar Salahuddin ɗauki, jaruntakar da Buzaye da ‘yan ƙabilar Kurɗawa suka nuna a wannan yaƙi yayi matuƙar bawa Larabawa mamaki.

Akan dole Raynaid na Chattilon ya juyar da akalar rundunar Kiristoci suna koma wa da baya, ba tare da samun nasara ba, suka bi ta ga ɓ ar ruwan Red Sea, suka sauya hanya. A wannan lokacin ne suka tare jiragen ruwan dake ɗauke da Musulmai ‘yan kasuwa da kuma Mahajjata inda suka ɗanɗana musu baƙar azaba, suka yi musu wasoso da kuma yi musu kisan kiyashi.

Labaran abubuwan da suka faru a wannan karon battar ya riski Manyan Sarakunan nan biyu masu wakiltar addinai. Richard ya yi matuƙar baƙin cikin rashin wannan nasara da Kiristoci sukayi na kasa kama Misira, inda ya sake shan alwashin ba zai cire sulkensa ba sai ya cimma burinsa na kare birnin Ƙudus kafin daga bisani ya isa Makka ya ɗanɗanawa Musulmai baƙar azaba.

Ɓ arnar da Raynald na Chatillon ya yi wa Musulmi a tekun (Red Sea) yayi matuƙar baƙantawa Salahuddin rai, domin wasu masana tarihin sun bayyana cewa, hatta ‘yar’uwarsa tana daga cikin waɗanda wannan lamari ya rutsa dasu.

Ba tare da  ɓ ata lokaci ba ya bada umarnin kar ɓ e iko da ga ɓ ar ruwan, sannan ya tashi jiragen ruwan guda talatiin inda ya umarce su da su kai ffarmaki birnin Beirut wajen da yayi tsammanin Raynaid da rundunarsa sun kafa sansani.

Manufar wannan farmaki shine kar ɓ e iko da mashigar ga ɓ ar ruwar kuma zata daƙike kuzarin Kiristoci da sake ratsawa ƙasashen Musulmai domin kai farmaki. Anci nasarar kar ɓ e iko da Beirut bayan kwashe lokaci mai tsawo ana gumurzu.

A yanzu Musulmai sun hara shanshanar birnin Ƙudus mai tsarki, sai dai mafarkin da suke na kama birnin tamkar haɗuwa ne da fatalwa cikin duhun dare..

Zan ci gaba a mako mai zuwa.

Exit mobile version