A wani sabon rahoto ya nuna yadda al’ummar jihar Yobe, dake Arewa Maso Gabashin Nijeriya suka nuna rashin gamsuwarsu da rashin sauke nauyin da ya hau wuyan kananan hukumomin jihar, tare da bukatar samun ingantuwar muhimman ayyukan raya yankunan karkara wanda ya rataya bisa wuyan kananan hukumomin.
Rahoton wanda aka yiwa taken: Rahoton Ayyukan Kananan Hukumomin Jihar Yobe, ya saurari ra’ayoyin al’ummar jihar dangane da tabbatar da gamsuwa ko rashin gamsuwa da ayyukan kananan hukumomin.
Sakamakon binciken, da aka fitar a ranar 18 ga watan Oktoba 2022, wanda kungiyar YMonitor ce ta gudanar dashi – wadda ke bibiya tare da tabbatar da ingantuwar tsarin Shugabanci da hadin gwiwa da kungiyar ‘The Future Project’ (TFP), wanda ya samu tallafin kungiyar ‘National Endowment for Democracy’.
A cikin takardar sanarwar da Shugaban dake jagorantar aikin YMonitor, Omidiji Olamilekan ya fitar yace, baya ga auna gamsuwar al’umma kan ayyukan kananan hukumominsu, rahoton har ila yau ya wayar da kan al’umma wajen sanin aikace-aikacen da suka rataya ga kananan hukumomin.
Bugu da kari kuma, binciken ya kunshi shawarwari ga hukumomi wajen farfado da tsarin kananan hukumomi a Nijeriya.
Haka kuma, jwabin nasa ya zayyano sakamakon binciken wanda ya bayyana yadda al’umma suka nuna rashin gamsuwarsu da Shugabannin Kananan Hukumomi, inda sakamakon binciken ya gano yadda jama’ar ke nuna tsananin damuwa a kan harkokin siyasa da kuma sanin ayyukan kananan hukumomin a tsakanin al’ummar jihar Yobe.
Jagoran wannan binciken, Omidiji Olamilekan ya ce, “Wannan rahoton zai taimaki shugabannin kananan hukumomi wajen gano matsayin da suke, amfani da damar da suke da ita wajen daukar matakan da ya dace don cike gibin da ake dashi cikin hanzari tare da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.”
Har wala yau kuma, ta hanyar amfani da na’aurar bincike ta ‘Net Promoter Score Test’, sakamakon binciken ya bayyana yadda jama’ar jihar Yobe suka ki amincewa da nada Shugabannin kananan hukumomin jihar zuwa wasu manyan mukamai na gaba.
Inda a karshe binciken ya bayar da shawarar cewa akwai bukatar gwamnati ta shirya tarukan karawa juna sani ga Shugabannin Kananan Hukumomi domin samun kwarewar zamani da duniya ke amfani dashi yanzu.