Shugaban sojojin Nijar, Abdourahamane Tiani, ya sanar da cewa Jamhuriyar Nijar za ta fara fitar da gangar danyen mai ta farko ta sabon bututun Nijar da Benin a watan Janairun 2024.
Tiani ya sanar da hakan ne a gidan talabijin na kasar a ranar Laraba.
- Hasashen Airbus: Sin Za Ta Kasance Babbar Kasuwar Hidimomin Sufurin Sama Zuwa Shekarar 2042
- An Shiga Firgici Bayan Sabon Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Kamfanin dillancin labarai na reuters ya bayar da rahoton cewa, a watan Nuwamban shekarar 2023 ne aka kammala aikin gina bututun mai da kamfanin makamashi na kasar Sin PetroChina ya yi. Wanda ya hada rijiyoyin mai na Agadem na Nijar zuwa tashar ruwan Cotonou na Benin.
A cewar Tiani, a halin yanzu an fara tura mai zuwa tankunan ajiyar da ke Cotonou, kuma ana sa ran komai zai daidaita nan da watan Janairu, wanda hakan ke nuna, farkon matakin kasuwancin mai na Jamhuriyar Nijar.
Nijar na da hakkin samun kashi 25.4% na ganga 90,000 na mai a kowace rana (bdp) da za a fitar da shi ta bututun mai.
Jamhuriyar Nijar ta na gudanar da wata karamar matatar mai, wacce ke da karfin tace mai kusan ganga 20,000 a duk rana.