Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya ta NSCDC reshen jihar Kano sun kama wasu mutane 11 da ake zargin barayin waya ne da dillancin kwayoyi a jihar.
Kakakin rundunar hukumar a jihar, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa manema labarai cewa, an kama wadanda ake zargin ne a lokacin sintiri na tsakar dare da jami’an tsaro na hadin gwiwa ke yi a jihar don yaki da masu kwacen waya da ta’ammuli da miyagu kwayoyi.
- Mutane 17 Sun Shiga Hannu Kan Hada-hadar Canjin Kudi Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano
- Gobara Ta Kone Wani Sashe Na Gidan Tsohon Gwamna Shekarau A Kano
Abdullahi ya ce, an kama wadanda ake zargin ne a Sabon Gari, Fagge, Kantin Kwari da Kofar Mata dauke da muggan makamai da wasu miyagun kwayoyi.
A cewarsa, ana kyautata zaton wadanda aka cafken, su ne ake zargi da addabar mazauna yankunan ta hanyar kwacen wayoyi daga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.