‘Yan sanda a Jihar Taraba sun yi ram da wani mutumin da dubunsa ta cika Bayan gano shi da laifin hada bama-bamai a Nijeriya.
An kama mutumin ne a garin Tella da ke karamar hukumar Gassol ta jihar a ranar Laraba.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an gano wasu kayayyakin hada bama-bamai, an kuma ga wasu bindigogi da harsashensu a gidan mutumin, wanda ya mayar masana’anta. Inji BBC Hausa.
Jami’an sun bayyana cewa, mutumin dan asalin Jihar Zamfara ne.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Usman Abdullahi ya tabbatar wa jaridar Daily Trust afkuwar lamarin da kama wanda ake tuhumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp