Akalla mutane 69 ne aka samu nasarar ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Bauchi sakamakon aikin hadin guiwa tsakanin jami’an tsaro da kungiyoyin sa-kai irin su ‘yan Bijilante da ‘yan Nanga wadanda suka kutsa kai maboyar masu garkuwan a cikin dazuka tare da ceto mutanen.
Wannan bayanin ya fito daga bakin kwamishinan kananan hukumomi da kula da Masarautun gargajiya na jihar Bauchi, Hon. Abdulrazaq Nuhu Zaki yayin da ke ganawa da ‘yan jarida a jiya.
Ya ce, tun lokacin da aka fara samun ‘yan matsalolin tsaro a jihar gwamnati da sarakuna hadi da jami’an tsaro tare da shugabannin kananan hukumomi suka bazama kokarin dakile aniyar bata-garin inda suka cimma muhimman nasarori kan hakan.
Ya ce, jami’an tsaron sun yi ta sintiri zuwa dazukan da ‘yan ta’addan ke fakewa inda suka fatattaki wasu tare da ceto wadanda suka yi garkuwa da su da dama.
A kan hakan ya ce yanzu jihar Bauchi ta samu kwanciyar hankali daga barazanar masu garkuwa da mutane, “Domin koda wasa gwamna Bala Muhammad baya sakaci da harkokin da suka shafi tsaro. Lamari na tsaro na faruwa zai tashi tsaye.”
A cewarsa an samu kwararowar ‘yan garkuwa da mutane cikin dazuka a Toro, Alkaleri, Tafawa Balewa da karamar hukumar Ningi wanda kuma tunin hukumomi suka yi abubuwan da suka dace domin dakile yunkurin su. Yana mai cewa wasu ma ba ‘yan jihar Bauchi ba ne.
A cewarsa: “Gwamna Bala Muhammad da kansa yake jagorantar yaki da wannan matsalar. Ya sha ziyartar yankunan da matsalar ya shafa tare da jajanta musu da kuma karfafa musu guiwar su dake su jajirce wajen tunkarar masu garkuwan daidai da karfinsu. Hakan ya kara wa jama’a kumaji da farkawa.
“Da hadin guiwar shugabannin kananan hukumomin jihar da shi kansa gwamnan Bala Muhammad da jami’an tsaro muna kan magance ‘yan kananan matsalolin tsaro da suke akwai. Domin shi gwamna bai wasa ko kadan a kan hidimar tsaro. Domin shi gwamnan ya karfafi masu ruwa da tsaki kan yin abun da ya dace.
“A wannan fatattakar da aka yi wa ‘yan ta’addan an samu nasarar kwato mutane 69 a sassa daban-daban na jihar Bauchi.”
Nuhu Zaki ya ce tunin gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya fara tattaunawa da Gwamnatin jihar Fitato da Taraba da suka iya iyaka da jihar domin ganin an hada kai wajen yin sintirin hadin guiwa domin kawo karshen ‘yan ta’addan da ke buya a cikin dazukan jihohin ukun.