Jami’an Tsaron Gidan Sanata Sun Lakada Wa Matar Aure Duka

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A ranar Juma’ar da ta gaba ne dai jami’an tsaro na ‘yan sanda masu gadin gidan Sanatan Bauchi ta Kudu Malam Ali Wakili suka lakkada ma wata matar aure dukan tsiya a sa’ilin da ta shiga gidan domin neman jakarta da ya bace. Lamarin ya biyu bayan tambayar jami’an ‘yan sandan ko sun ga jakar nata ne, inda wani dan sanda ya yi mata dukan tsiya duk da tana dauke da juna biyu.

Matar mai suna Balkisu Muhammad ta kawo kukanta ofishin ‘yan jarida inda ta yi bayanin lamarin kamar haka “Mun fito ranar alhamis da ni da wasu mata biyu, daya daga cikinmu ta ce muje mu yi sallah a gidan kawarta, mun hadu da matan ne wajen neman tallafin bada rance da ake yi, muna kokarin cika sharuddan da ake nema kenan, sai lokacin sallah ya yi, matar sai ta ce muje gidan kawarta sai mu yi sallah. Mun shiga gidan muka zauna wacce muka zo neman ma bata nan hakan ya sa na ce wa matar mu fita bata nan sai na ce musu su tashi mu tafi tunda dan sandan ya je ya tambaya an ce bata nan”

Balkisu ta ci gaba da cewa “Bayan da muka fita mun shiga keke napep sai na lura na mance jakata a gidan, a cikin jakar akawai katin shaida ni dalibace, da kuma takardar wannan kungiyar da sauran katinana da suke ciki, haka kuma da akwai kudi har dubu biyar a cikin jakar, bayan da muka yi nisa sai na laluma na ji babu jaka, muka yi kokarin komawa amma mun yi nisa da gidan kuma babu kudin da zai kaimu gidan”. A cewarta

Ta ce, hakan ne ya sa suka hakura da komawa, inda ta shaida wa mijinta domin ya maida ita gidan domin duba jakar nata, a yayin da shi kuma ya bukaci ta bari sai washe gari, juma’a kenan inda a nan ne tsautsayin ya rufta mata “bayan da na je gidan na yi sallama na tambayi jami’an tsaron da suke gadi na ce musu don Allah na jiya mun zo nan na mance jakata ko Allah ya sa sun gani, sai wani Sajen din dan sanda mai suna Albat Baba ya shaida min cewar bari ya tambayi sauran abokan aikinsa, bayan ya tambayesu kowa ya ce bai gane ni ba; na shaida masa cewar ni fa ba wai ina zuwa kullum bane jiya ne kawai muka zo da wasu kawaye na biyu. Daga nan sai ya ce min gaskiya babu wani abu da kika mance mu bamu gani ba. ina kokarin fita daga cikin gidan ne kawai sai wani dan sanda mai suna Jonathan Bangus yana daga wani sashi daban na cikin gidan ya fito bai san hawa ba bai kuma san sauka ba ya kama dukana da bakin bindigarsa, yana ce min go out”. A cewarta

Ta ce, a karin farko ya daketa a cikinta ne inda take dauke da cikin wata biyar wannan dalilin ya sa ta yi kokarin kare cikin nata kada ya sallawanta “dukan da ya min na farko sai na fadi kasa, ya dokeni da bakin bindigarsa, sai da na fadi, na yunkura zan tashi ya saitani da bindiga kamar zai harba sai shi wannan Baban dan sandan ya ke fada masa da turanci macece fa! Ai kuwa sai ya dawo ya ci gaba da dukana, ya jimin ciwo a hanu da kuma fuskana, ya kuma dokeni a wurare da dama har da  cikina duk da ina dauke da juna biyu na wata biyar”.

Bilkisu ta ce  bayan da sauran ‘yan sanda musulmai suka lura yana neman wuce gona da iri ne wasu daga cikinsu suka yi kansa suka kwantar da shi da yunkurisun na kwace bindigar hanunsa don kada ya kasheta “Bayan da Allah ya taimakeni sai na fita daga gidan na rarrafa na je ofishin ‘yan sanda da ke GRA domin kai kukena domin na firgita kada ya zama cikin da nake dauke da shi kada ya zube ko wani abun daban”.

Ta ce dan sandan ya ki bada hadin kai ko bayan da suka je da wani dan sanda daga caji ofis domin bincike amma basu samu hadin kai ‘yan sandan gidan Sanata Ali Wakilin ba. ta ce ya zuwa yanzu babu wani mataki da aka dauka na kwato mata ‘yancinta da keta mata haddi da jami’an ‘yan sandan suka yi duk da kasancewarta matar aure kuma musulma “Tun shida nake ofishin ‘yan sanda har goma da rabi na dare suka ki saurarona sai da na ce musu gaskiya ni zan tafi, daga baya suka ji korafina. Mijina ya nemi su taimakamin domin kaini asibiti suka ki, shine a cikin dare ya kaini aka duba lafiyata. Tun da suka dauki jawabina har yau ban sake jin wani yanemi don haka zalumcin yayi yawa, a bisa haka ne muka tashi domin neman hakkina”. In ji ta

Ta ce mijinta ya ce bai yarda ba don haka zai nemi hanyoyin da suka dace domin kai kukansa da kuma neman hakkinsa daidai da shari’a.

Matar da ‘yan sandan gidan sanatan suka dakada wa duka ta gabatar wa wakilinmu rahoton gwaje-gwajen da aka yi mata a asibitin Reemee domin tabbatar da cewar dukan ko ya shafi dan cikin nata ko akasin hakan, inda rahoton asibitin ya daura matar kan wasu ka’idojin da in ta bi da yardar Allah dan cikinta ba zai samu matsala ba. inda kuma suka bata magunguna da sauran kulawa domin tabbatar mata da lafiyarta.

Balkisu Muhammad ta nemi dukkanin wasu kungiyoyi da kuma hukumomin kare hakkin mata da su taimaka mata su bi mata haddinta da kuma binciken hakikanin abun da ya faru domin hana zalumci hauhuwa a fadin kasar nan.

DSP Kamal Datti Abubakar shi ne mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ya shaida wa wakilinmu cewa zai bincike labarin domin jin hakikanin abun da  a faru a tsakanin jami’ansu da kuma matar auren. Ya zuwa aiko da labarin nan bai gama bincikowar ba.

Exit mobile version