Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa jami’an tsaro sama da 100 sun mutu yayin da suke ƙoƙarin kare jihar daga ‘yan ta’adda.
Kwamishinan tsaro na jihar, Nasir Mua’zu, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai sama da ‘yansanda 30 da kuma wasu sojoji.
Ya ce dukkansu sun mutu ne a bakin aiki domin kare lafiyar mutane da dukiyoyinsu.
Mua’zu ya ce gwamna Dikko Umar Radda yana ƙoƙari sosai wajen ganin an magance matsalar tsaro, inda ya kafa ƙungiyoyin ‘yan-sakai da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da jami’an tsaro.
A cewarsa, lokacin da gwamnan ya hau mulki, ƙananan hukumomi 24 suna fama da matsalar ta’addanci.
Amma yanzu, babu matsalar gaba ɗaya a ƙananan hukumomi 11, yayin da aka samu sauƙi a wasu tara.
Ya ce har yanzu ana fama da hare-hare a ƙananan hukumomi huɗu: Faskari, Ƙankara, Safana da Matazu.
Kwamishinan ya jaddada cewa jami’an tsaro suna iyakar ƙoƙarinsu, kuma gwamna yana ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar.
Ya buƙaci al’umma da su daina suka, su kuma tallafa wa jami’an tsaro da addu’a da fahimta, ganin irin sadaukarwar da suke yi domin kare rayukan jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp