Ranar Litinin ce mataimakin shugaban jami’ar Ajayi, Farfesa Timothy Adebayo Timothy Adebayo, ya ce babbar matsalar da take damun ilimi a Nijeriya ita ce rashin isassun kudaden da za’a tafiyar da shi ilimin.
Adebayo ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taro lokacin da aka yi bikin yaye dalibai na Jami’ar na 16 a Oyo Jihar Oyo.
- Jami’in Yada Labarai: Kasar Sin A Shirye Take Ta Aiwatar Da Hadin Gwiwar Kasashe Na Hakika Tare Da Mambobin G20
- Jami’i: Kofar Sin A Bude Take Domin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa Da Amurka Don Inganta Dangantakar Tattalin Arziki Mai Daidaito
Ya ce matslar bata tsaya kadai bane kan Jami’oi masu zaman kansu, saboda akwai na Jiha da gwamnatin tarayya, da suke kara kudaden karatu saboda hakan ne zai taimaka musu tafiyar da harkokinsu da suka shafi kudade.
Ya kara jaddada cewa, “Rashin samun damar isassun kudade hakan yana nufin yawan manyan makarantu da kyar suke samar da abubuwan da suka zama dole na dakin gwaji, da sauarn wasu abubuwan more rayuwa da ake bukata saboda bunkasar ilimi a Nijeriiya.
“Kana iya magana kan gidauniyar tallafawa manyan makarantu na amince ta taimakawa ilimi kwarai da gaske,sai dai kuma siyasar da take tattare da yadda take fitarwa da bada kudade, hakan bai sa gidauniyar ta yi wani abin azo a gani ba a bangaren ilimi.
“Ba abin mamaki bane yadda Jami’oi masu zaman kansu suke kara kudin makaranata kai har ma na gwamnatoci suna kara kudaden, duk kuwa da yake akwai hukumar ko gidauniyar TETFUND bada taimako kawai saboda su yi bayani yadda suke kashe kudaden, wannan ya nuna yadda irin Jami’oin suke ta fadi- tashi kan lamarin da ya shafi kudi.”
Mataimakain shugaban jami’ar ya ce ACU ta samu ci gaba ta bangaren ilimi da kuma yadda take a shekarun baya da suka wuce,inda ya bayyana cewa jami’ar gaba take da fara yin tsarin karatu a gida.
“Jami’ar tana yin duk abubuwan da za ta iya domin ta samu damar bullo da cibiyar tsarin karatu a gida ODL domin ta kara samar da hanyoyin da wasu mutane wadanda ke fuskantar matsala wajen samun damar zuwa manyan makarantu domin kara ilimi kamar yadda ya jaddada’’.
Da yake bayan ikan ire- iren abubuwan karatun daya samar a shekaru hudu da suka gabata ga wadanda ya tarad , Adebayo ya ce an kara samar da kayayyaki aiki 29, yayin da kuma Jmi’ar ta fara tsarin musayar dalibai da makarantu 15 a cikin gida da kuma wajen Nijeriya.
Daga karshe ya ce za’a b awasu mutane,2,679 takardun shedar kammala Jami’a a bikin yaye dalibai na wannan shekarar inda 86 suka samu digiri mai daraja ta daya.