Jami’ar Nsukka (UNN) ta ƙaryata cewa ta taɓa bai wa Uche Nnaji, Ministan Kirkira, Kimiyya da Fasaha na Shugaba Bola Tinubu, takardar shaidar kammala digiri.
Rahotannin da jaridar Premium Times ta samu sun nuna cewa Nnaji ya yi iƙirarin cewa ya samu digirinsa daga jami’ar.
- Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci
- Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno
Amma jami’ar ta ce ba ta da wasu bayanai da suka nuna cewa an taɓa karɓarsa ko ya kammala wani sashe a jami’ar.
Jami’an jami’ar sun tabbatar cewa takardar shaidar da aka danganta da su ba ta da inganci, inda suka gano bambance-bambance a tsarin rubutu, lambar ɗalibi da kuma alamar tsaro idan aka kwatanta da takardun asali na jami’ar.
Haka kuma, wasu ma’aikatan jami’ar, na baya da na yanzu sun tabbatar da cewa ba su da wani bayanin da ya nuna Nnaji ɗalibi ne da ya taɓa yin karatu a can.
An kuma ce duk wani bincike da aka yi a sashen karatu da kundin tsofaffin ɗalibai bai nuna sunansa ba.
Wannan binciken ya jefa shakku kan sahihancin takardun ilimin ministan, tare da tayar da ƙura kan yadda gwamnati ke tantance waɗanda ake bai wa manyan muƙaman gwamnati.
Duk da cece-ku-ce da ake yi, har yanzu Nnaji bai mayar da martani ba, haka kuma fadar Shugaban Ƙasa ta ƙi ta ce komai kan lamarin.
Wannan na zuwa ne a lokacin da ake tambaya kan yadda ake ɗaukar nauyin masu riƙe da muƙamai a gwamnatin Tinubu, musamman kan tsarin tantancewa kafin a ba su manyan muƙamai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp