Yayin da jam’iyyar MPR Jamhuriya ke bikin cikar shekaru biyu da kafa ta, shugabanta, Albade Abuba, yayi kira ga ‘yan adawa da masu rinjaye su manta da banbancin siyasa domin su kuɓutar da ƙasar daga halin fatara da matsalar tsaro.
A jajiberen zaben 2016 ne wasu jigajigan jam’iyyar MNSD suka kafa jam’iyyar MPR Jamhuriya bayan da suka yi shekaru biyu suna tafka shari’a tsakanin masu goyon bayan shugaban ƙasar Issoufou Mahamadou da waɗanda suke adawa. Yayin da jam’iyyar ke cika shekaru biyu da kafuwa, shugabar matan jam’iyyar, Madam Lamido Salamatu Bala Goga ta ce jam’iyyarsu ta taka rawar gani saboda watanni uku da kafa ta ta shiga zaɓen ɓasa har suka ci kujeru 13.
A bikin nata, jam’iyyar ta gayyato shugabannin siyasar ƙasar baki ɗaya lamarin da ya ba shugabanta Albade Abuba damar kiransu da su kawar da banbancin siyasa su haɗa kai domin yaƙar matsalolin da ƙasar ke ciki yanzu irinsu fatara da taɓarɓarewar tsaro.