Bello Hamza" />

: Jam’iyyar APC Da PDP Sun Taya Ma’aikatan Nijeriya Murna

Daga Bello Hamza

 

Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan ta mika sakon gaisuwa da fatan alhairi ga illahirin ma’aikatan kasar nan a bisa bikin ranar ma’aikata na duniya na wannan shekarar “May Day celebration”.

Jam’iyyar APC ta bayar da wannan sanarwar ne ta hannun jami’in watsa labaranta Alhaji Bolaji Abdullahi, ya ce, ma’ikatan Niheriyab sun kasance jagora a fagen ci gaban kasar nan duk da dinbin matsalolin da suke fuskanta.

“Tabbas ma’aikatan Nijeriya na daga cikin ma’aikata masu aiki tukuru da kula da aiki a duniya, sun kasance jagora a kokarin da ake yi na bunkasa tattalin arzikin waannan kasa namu mai kafar tattalin arziki mai yawan gaske.

“Duk da matsalin da ake fuskanta na tattalin arziki, muna alfahari da ma;aikatan Nijeriya saboda jajircewarsu wajen hada hannu da gwamnati domin gina kasa duk da matsalolin da ake fuskanta, ma’aikata na kokari kwarai da gaske domin kai kasar nan gurbinta daya dace”

Jam’iyyar APC ta kuma bukaci kungiyoyin kwadago dasu ci gaba da tattaunawa da gwamnati da nufin kara albashin ma’aikata da jin dadinsu gaba daya.

Haka ita ma jam’iyyar adawa ta PDP ta taya ma’aikata Nijeriya murnar wannan rana na ma’aikata ta duniya, ta bukaci ma’aikatan Nijeriya dasu jajirce wajen tabbatarbda mulkin dimokradiya su kuma kauce wa karya doka da katsalanda da gwamnatin dake ci a yanzu ke yi wa harkokin ma’aikata a kasar nan.

“Dole ma’aikatan Nijeriya su yi Magana da muryab daya wajen kalubalantar cin zarafin yan Nijeriya da kuma halin ko in kula na gwamnatin Muhammadu Buhari musa,mman kasha-kashen da ake yi na ‘yan kasa a wurare irinsu Biniwai da Kaduna da Kogi da Nasarawa da Yobe da Borno da Plateau da kuma jihar Zamfara da kuma sauran sassan kasar nan da ‘yan ta’adda ke cin karesu babu babbaka.

“Dole kungiyoyin kwadago su kalibalanci salon mulkin gwamnatin Buhari da tsananin cin hanci da rashawa da yayi katutu a gwamnatin abin ke daya kai ga tabarbarwewar tattalin arzikin tare da asarar aiyukan mutane fiye da Miliyan 24 da kuma tsananin wahala da yunwa da talauci da fatara da kasar ‘yan NIjeriya ke fuskanta a halin yanzu.

“Haka kuma muna kara kira ga rundunar ma’aikatamu dasu tasji tsaye domin kare mulkin dimokradiyya musamman karya dokoki da katsalanda a cikin aiyukan bangaren majalisar kasa da na shari’a da kuma musgunawa ‘yan adawa abin daya zama rowan dare a wannna gwamnatin. Inji PDP

A wani sako kwatankwacin wannan kuma, shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, ya tabbatarb wad a ma’aikata Nijeriya cikakken goyon majalisar dattijai a wannan lokaci, a sanarwa data fito daga ofishinsa ranar Litinin, ya jinjina wa ma’aikatan Nijeriya a bisa jajircewarsu da aiki tukuru da kuma gudummawarsu ga bunkasar tattalin arzikin kasar nan.

Ya yi wannnan bayanin ne a cikin sakonsa na murnar ranar ma’aikata na duniya da jam’in watsa labaransa, Yusuph Olaniyonu, ya sanya wa hannu, ya ce, ma’aikata sune kashen bayan bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.

Ya yi alkawarin cewa, majalisar dokoki a karkashensa zata goyi bayan duk wani matakin da zai tabbatar da ma’aikata na samun kulawar daya kamata a dukkan fannonin rayuwa. Ya bukaci ma’aikata dasu ci gaba da himma da kokari a dukka bangaren da suka samu kansu, su kuma sani cewa kokarinsu ba zai taba tafiya a banza ba.

“Ba za a taba samun ci gaba tattalin arzikin ksa ba tare da gudummawar ma’aikata bah aka kuma mba za a taba samun ci gaban kasa ba ba tare da bunkasar tattalin arziki ba. Sanata Saraki ya kara da cewa, “ma’aikatnmu sun bayar da gudummnawa mai matukar mahimmanci a dukkan nasarorin da muka samun a matsayinmu na kasa, saboda haka dole mu san da haka a kowanne lokaci”

“A wannan bikin ranar ma’aikatab na shekarar 2018, ina jinjina ga ma’aikatan Nijeriya a bisa sadarkarwasu da jajircearsu duk da matsaloli da koma bayan tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta.”

Shugaban majalisar dattijain ya hori ma’aikata dasu ci gaba da taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da kasa baki daya, ya kuma kara da cewa, “Majalisar kasa zata mika goyon baya ga duk wani kokarin an kara albashi da inganta rayuwar ma’aikatan Nijeriya.

“Ma’aikata ne ginshikin tattalin arzikin kasa, in har babu su to babu wani harkar tattalin arzikin da zai tafi dai-dai ta kowacce fuska” inji shi.

Haka kuma, Ministan kwadago da samar da aiyukan yin a kasa, Mista Chris Ngige, ya yaba wa ma’aikatan kasar nan a bisa jajircewarsu, ya kuma tabbatar musu da cewa, ana nan ana tattaunawa a kan yanke shawarar karancin albashi ga ma’aikacin kasar nan.

A sakon fatan alhairi a bisa bikin ranar ma’aikata na duniya daya aika wa ma’aikatan Nijeriya,Ministan ya tuno da irin kokarin da ma;aikatan suka a tsawon shekaru, ya kuma bukace su dasu tsaya tare da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Mr Ngige ya kara da cewa, babban manufan wannan gwamnatin shi ne farfado da tattalin arzikin kasa da tabbatarbdac tsaro a kasa da kuma kakkabar da cin hanci da rashawa. Ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya ta yi gaggarumin kokari a wadannan fannonin.

A saboda haka sai ya nemi goyon bayan ma’aikata Nijeriya ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari domin cimma wannan buri namu da yardarm Allah.

Mininstan ya kuma tabbatar wad a ma’aikatan cikakken kudurin shugaba Buhari domin bunkasa rayuwar ma’aikata a dukkan lokaci. Ya kuma bukaci dasu yi amfani da gwagwarmayar kungiyar su a wadago wajen kwato ‘yancin ma’aikatan Nijeriya baki daya.

“Wannnan gwamnati ta sanya lamarin hakokin ma’aikata dana sauran yanNijeriya da matukar mahimmanci, tana kuma gudanar da kokarin cimma wannan burin ne ba tare da wani boye boye ba. babban nurinmu shi ne samar da yanayin da dukkan ‘yan Nijeriya zasu daman bayar da gudummawarsu yadda ya kamata tare da mutunta kokarin da gwamnati ke gatararwa.

“Alamun nasarar da muka samu wajen samar da yanayin tsaro ga aiyukan ‘ya Nijeriya da bayarb da dama ga dukkan ‘yan nijeriya ba tarebdacnuna banbanci ba shi ne babu wani ma’aikacin gwamnatin tarayya daya rasa aikinsa a cikkn shekara 3 da suka wuce duk da matsin tattalin arziki da muke fuskanta. Haka kuma kokarin da gwamnatin tarayya ke yin a samar da sabon albashi mafi karanci domin daukaka rayuwar ma’aikata Nijeriya, alami ne dake nuna fatanmu ga ma’aikatan Nijeriya.

Ranar ma’aikata “Workers’ Day” ko kuma “May Day” ko “Labour Day” ran ace da ake hutu a Nijeriya da sauran wasu kasashe a duniya, gwamnatin jam’iyyar PRP ta jihar Kano c eta fara aiyana ranar a shekarar 1980 daga baya ya zama ranar hutu ta kasa a ranar 1 ga watan Mayu na shekarar 1980.

 

 

Exit mobile version