Jam’iyyar LP ta gargadi jam’iyyar APC kan sukar da mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, sanata Kashim Shettima ke yiwa dan takarar shugaban kasarta, Peter Obi da sauran ‘yan takarar shugaban kasa akan zaben 2023.
Daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar LP, Dakta Doyin Okupe ne ya yi wannan kiran ga APC, inda ya yi nuni da cewa, kalaman Shettima, sun sabawa yarjejeniyar da jam’iyyun siyasar kasar nan suka rattaba hannu kan dokokin yakin neman zabe cikin lumana.
Doyin ya ce, sun gani a cikin bacin rai yadda yakin neman zaben din batanci da Shettima ke yi wa Obi da sauran ‘yan takarar shugaban kasar.
Ya ci gaba da cewa, daukacin jam’iyyun sun rattaba hannun yarjeniyar yin yakin neman zabe a cikin zaman lafiya wacce tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janar Abdulsalami Abubakar mai murabus ya jagoranta da aka gudanar a kwanan baya a Abuja.
Doyin ya sanar da cewa, tawagar yakin neman zabe ta jam’iyyar LP na son ya shawarci jam’iyyar APC da ta gargadi Shettima akan salon sa na yakin neman zabe na batanci da ya ke yiwa Obi da sauran ‘yan takarar shugaban kasa a kakar zaben 2023.