Connect with us

LABARAI

Jam’iyyar PDP Ta Shirya Tsaf Don Kafa Gwamnati A Jihar Kano A Zaben 2019

Published

on

An bayyana cewa, in har dan takarar Gwamnan jihar Kano a tutar jam’iyyar PDP Hon. Sadik Wali ya samu nasara a zaben 2019 dake tafe zai kawo wa jihar Kano ainihin canjin da al’ummar jihar ke bukata wajen samar da ababen more rayuwa.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin babban darakta janar na yakin neman zaben Sadik Bashir Wali a matsayin gwamnan jihar Kano Hon. Yahaya Bagobiri, ya fadi haka ne a wani taro da daraktocin suka kira domin fadakar da ‘yan jam’iyyar ta PDP, musamman masu fitowa kafafen yada labarai ko social media kan su guji kalaman batunci ko tayar da rigima a kan duk wani dantakara.
Yahaya Bagobiri ya ce, duk dan PDP a jihar Kano da kasa baki daya dasu zamanto masu kara zamantowa masu natsuwa da kuma kishin jam’iyya tare da yi mata baiyayya. Alhaji Yahaya ya ce, matukar Sadik Wali ya samu nasara zai yi bakin kokarinsa wajen kawar da tarin matsalolin da ke addabar al’ummar jihar kamar rashin aikin yi ga matasa rashin kyawawan hanyoyi, tare da rashin magunguna a sibitocin jihar. Ya koka matuka game da yadda aka san jihar Kano da masana’antu daban daban amma rashin kulawa ya sa yawancin masana’antun jihar duk sun durkushe sakamakon rashin hasken wutan lartarki.
Darakta janar din ya ce, ‘yan PDP na jihar Kano da kasa baki daya su tabbatar ranar zabe sun zabi PDP tun daga kasa har sama. Sannan a matsayinsa na darakta janar din yakin neman zaben na Sadik Wali, da sauran daraktoci zasu yi bakin kokarisu wajen tallata manufofi da kyawawan kudirin da mai neman gwamnan yake da shi a daukacin kananan hukumomin jihar Kano 44, ya ce, alamu sun nuna cewa al’umma musamman matasa masa maza da mata na tare da kiran na Sadik Wali
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: