Daga Bello Hamza,
Jam’iyyu 12 suka gabatar da ‘yan takara a zaben kananan hukumomi da za a gabatar a jihar Kano ranar 16 ga watan Janairu.
Shugaban hukumar zabe na jihar, Farfesa Ibrahim Garba-Sheka, ya bayyana haka a tattauwarsa da manema labarai a garin Kano ranar Asabar.
Garba-Sheka ya ce, hukumnar ta kammala dukkan shirye-shirye na ganin an gudanar da sahihin zabe kamar yadda dokar zabe ta tanada a fadin jihar.
Ya ce, hukumar ta gana da shugabanin jam’iyyar don shirya yadda za a gudanar da zaben.
“Tuni muka fara raba kayyain zabe a yankunan kananan hukumomin don cigaba da gudanar da zaben.
“Haka kuma mun horas da ma’aikata na wucin gadi don sanar dasu yadda za su gabatar da aikin su yadda ya kamata.
“Nasarar zaben nan aiki ne na dukan al‘ummar jihar akan haka muke neman goyon bayan kowa da kowa don ganin an gudanar da sahihin zabe,” inji shi.
Akan haka Farfesa Garba-Sheka, ya bukaci jam’iyyun siyasa su samar da yadda za su lura da yadda za a gudanar da zaben a fadin jihar, an kuma samar da masu lura da zaben har kungiya 200 da za su shigo jihar su lura da yadda za a gudanar da zaben.