Samun nasarar kowace gwamnati sun ta’allaka ne game da irin nagartattun jami’anta wadanda aka zaba ko aka nada. Shugabannin gwamnati sukan zabo hazikan mutane maza da mata domin tafiyar da sassa daban-daban na tattalin arziki a matsayin ministoci ko sakatarori, su ne ke jan ragamar dukkan daukacin tsarin gwamnati.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullun sun bayyana cewa gwamnatin tsohon gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaza ne a wasu bangarori sakamakon ministocin da ya hada.
Tinubu a lokacin yakin neman zabensa ya yi alkawarin bayyana sunayen ministocinsa watanni biyu idan ya zama shugaban kasar. Sannan ya yi alkawarin zakulo nagartattun mutane maza da mata da zai hada a mukamin ministoci wadanda suka gogewa, da za su taimaka wajen samar da ayyukan ci gaba a kasar.
A yanzu haka ya ture da sunayen wadanda zai bai wa mukamin ministoci kuma har majalisa ta tantance su, ban da mutum uku.
Ko shakka babu daga cikin mutanen akwai wadanda suka cancanta, sannan kuma wasu ‘yan Nijeriya na shakku game da wasu daga cikin mutanen, musamman tsofaffin gwamnoni.
Mistoci ne ke jan ragamar jagorancin tafiyar da ma’aikatun gwamnati, wanda a halin da ake cikin a Nijeriya ma’aikatun suna neman agaji wajen tafiyar da shugabanci domin tunkarar kalubalen da ke fuskantar kasar nan.
‘Yan Nijeriya na ci gaba da kokawa sakamakon mawuyawacin halin da suka shiga, musamman ma a daidai lokacin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta cire tallafin mai ta yadda matsin rayuwa ta lunka.
Masana na ganin cewa babbu wani bangare na ma’aikata da cin hanci bai je ba wanda hakan ya hana gudanar da abubuwa yadda suke.
Lallai akwai jan aiki a gaban ministocin Tinubu wajen neman hanyar da za su iya bi domin dinke farakar da ke addabar ma’aikatun Nijeriya, musamman ma wadanda suka da dangantaka da harkokin kudade.
Za a iya sake fasalin Nijeriya ne kadai idan aka gudanar da abubuwa yadda kundin tsarin mulki ya ayyana ba tare da son zuciya ba.