Nada Tsohon Hafsan Sojin Rundunar Tsaron Kasar nan Janar Christopher Musa mai murabus, a mukamin Babban Ministan Tsaro, hakan na kara janyo yin tsokaci, musamman a kafafen yada Labarai.
Wasu da dama na yin hasashen cewa, nadin na sa, ya zo a kan gaba musamman duba da cewa, a wannan mulkin na Demokiradiyya ne, aka fara samun nada, tsohon babban hafsan soji,a mukamin na babban ministan tsaro, kasar jim kadan bayan ya yi murabus.
- Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Farfesa Ibrahim Tsafe A Matsayin Sabon Shugaban Jami’ar ZAMSUT
- Sin: An Kaddamar Da Manufar Kafa Hidimar Kwastam Mai Zaman Kanta A Tsibirin Hainan
Masu ruwa da tsaki da dama, sun yi maraba da nadin wanda hakan ya nuna cewa, wani babban mataki ne, na nufin magance kalubalen rashin tsaro da kasar ke ci gaba da fuskanta.
Kazalika, ita ma wannan Jaridar, ta bi sahun ra’ayin wadannan masu ruwa da tsakiin wajen yin maraba da nadin na Musa musamman idan aka yi la’kari da irin kwarewa da bisirarsa, da ya samu a gidan soja.
Sai dai, wannan Jaridar na ganin wannan nadin na sa, cike yake da babban nauyi da aka dora masa wanda kuma bai da wata dama, ta gabatar da uzuri, kan wannan nauyin da zai iya bayarwa, wajen sauke nauyin.
Mutane da dama dai, na ganin bai kamata ace. Musa ya gaza sauke wannan nauyin ba, musamman ganin cewa, a matsayin na tsohon babban hafsan soji, ya san duk wani shige da fice, da zai yi, domin kawo karshen kalubalen na rashin tsaro, da ya yiwa kasar kakatutu.
Tabbas, nauyin da ke a Kansas, ba karami bane, musamman duba da cewa, a lokacin da ‘yan majalisa ke tabtance shi a zauren majalisa, ya zayyano wasu daga cikin manyan matsalolin, da yake son ya tunkara kan matsalar ta rashin tsaro.
Matsalar daya da ya kamata Musa a yanzu ya tunkara ita ce, ta bazuwar makamai ba bisa ka’ida ba, a hannun wasu alumomin kasar, wadda kuma ake ganin ke janyo cikas na gudanar da ayyukan sojin kasar.
Kazalika, wannan Jaridar, na ganin ya kuma zama wajibi sabon babban ministan tsaron ya tabbatar da an wadata dakarun sojin kasar da kayan yaki yadda za su tunkari duk wani kalubalen rashin tsaro a kasar.
A shekarar 2024 ne dai, Nijeriya ta rattaba hannun yarjejeniyar da hukumar kera makamai ta kasa wato NASENI tare da kuma ma’aikatar tsaro ta kasa,domin a kera makamai da kuma kula da su, inda wannan Jaridar na ganin cewa, wannan mataki ne da ya dace matuka.
Bugu da kari, wani babban abin sha’awa shi ne, sabon babban ministan tsaron, a baya ya kadsncr a kan gaba wajen ssmar da dimbin dsbarun da za a bi, domin lalubo da mafita kan lamarin matsalar tsaro a kasar nan.
Hakan ne ya sanya, a lokacin da ya ke rike da mukamin na babban hafsan tsaro na soji, ya shirya taron manyan hafsoshin soji na nahiyar Afirka wanda aka gudanar a Abuja.
Taron ya samu halartar manyan hafsoshin soji guda 37, da suka fito daga nahiyar Afirka, musamman a lokacin taron sun tattauna kan yadda za a magance matsalolin rashin tsaro a tsakanin kasashen Afirka
A jawabin da ya gabatar a wajen taron, a lokacin yana rike da mukamin na babban hafsan rundunar tsaron kasar Musa ya bayyana cewa, lokacin kawo kasashen kalubalen rashin tsaro da nahiyar Afirka ke fuskanta ya zo karshe kuma dole ne, mu tashi haikan, wajen tsayawa tsayin daka, domin tunkarar matsalar ta hanyar samar da kudaden fa za a yi aiki domin bai kasashen mu, kariyar da ta kamata.
A namu ra’ayin kan wannan furucin na sabon babban ministan tsaron, tamkar umarni ne na tabbatar da an samar da wadataccen tsaro.
Kadancewar a yanzu Christopher Musa ne ke rike da mukamin na babban ministan tsaron kasar nan, hakan zai ba shi, yin amfani da karfin ikon da yake da shi wajen wanzar da wannan tsarin na sa, ba tare da bata wani lokaci ba.
Akwai bukatar a mayar da hankali a bangaren samar da tsari da kuma tabbatar da an wanzar da tsarin, ba tare bata wani lokaci ba.
Hakazalika, akwai nauyi a kan ma’aikatar tsaro wajen bayar da shawarin da sika shafi fannin gudanar da mulki da bayar da goyon baya akan lokaci wanda hakan zai bai wa rundunar sojin kasar gudanar da ayyukan ta, yadda ya kamata.
Wannan wani nauyi ne babba da aka dorawa sabon babban ministan tsaron kuma mai kunshe da sarkaiyar wandarwa.
A matsayin mu a wannan Jaridar, muna da yakin cewa, a yanzu rundunar sojin kasar a shirye take domin tunkarar duk wata barazanar rashin tsaro da kasar ke fuskanta. Fadin namu na hakan na zuwa ne, musamman dangane da irin labarukan da muke wallafawa na ci gaba a fannin tsaro na kasar nan da kuma irin fashin baki da muke yi, kan lamarun yau da kullum na kasar nan.
Babbar shawarar ga sabon babban ministan tsaron ita ce, kar ya daga kafa wajen kawo karshen kalubalen rashin tsaro a kasar, musamman duba da cewa, daukacin ‘yan kasar, sun jima da gajiya da batun na kalubalen na rashin tsaro.
Wannan Jaridar, na da kwarin guwair cewa, sabon babban ministan tsaron ba da duk wata kwarewar da ake bukata, domin sauke nauyin da aka dora masa.














