Masana da masharhanta da masu bin diddigin al’amuran da ke wakana a game da huldar kasar Sin da Afirka sun kasa kunne, sun zuba ido suna tsumayar abubuwan da taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC zai kunsa musamman a wannan karo da dandalin ke cika shekaru 24 da kafuwa.
Da yake ni dan Afirka ne, hankalina ya fi karkata a kan abin da zai fito daga bangaren kasar Sin, saboda yadda har yanzu muke fama da gibin kayayyakin more rayuwa da ci gaban tattalin arziki. Na bibiyi jawabin da Shugaba Xi Jinping ya gabatar na bude taron, inda na yi kicibis da abubuwa masu kara kwarin gwiwa game da kudurin kasar a kan Afirka, da yake nuna gaskiyarta wurin hulda da mu’amala da su har ta zama baya-goya-marayu a gare su.
- “ChinaTravel” Ya Fahimtar Da Al’ummar Duniya Hakikanin Yanayin Da Ake Ciki A Kasar Sin
- CHINADA Ta Nuna Shakku Ga Hukuncin Da Aka Yanke Kan Dan Wasan Tsalle-tsalle Da Guje-guje Na Amurka Game Da Shan Maganin Kara Kuzari
Abin da ya fi jan hankalina daga jawabin shi ne albishirin da Shugaba Xi ya yi wa Afirka na cewa kasarsa ta kimtsa tsaf domin aiwatar da wasu matakai na kawance guda 10 cikin shekaru uku kacal domin cimma burin zamanintar da kasashen. Sassan da za su ci gajiyar hakan sun hada da koyi da juna ta fannin wayewar kai, bunkasa kasuwanci, ci gaban masana’antu, hadewa da juna, hadin gwiwar samun ci gaban juna, kiwon lafiya, aikin gona da kyautata rayuwar jama’a, mu’amalar al’umma da musayar al’adu da kuma tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da al’amuran tsaro.
Wadannan abubuwa ba kawai suna da muhimmanci ba ne ga ci gaban nahiyar Afirka, za su kuma taimaka wa kasashen yankin su kara fahimtar kawunansu don tsayawa da kafafunsu domin har yanzu akwai burbushin mulkin mallakar Turawan yamma cikin tsarin tafiyar da shugabanci da tattalin arzikinsu a fakaice.
Har ila yau, Shugaba Xi ya nuna yadda kasar Sin ke aiwatar da kawance da Afirka cikin ’yan uwantaka, yayin da a jawabin nasa ya yi kiran zurfafa ci gaban zamani mai adalci ga kowa ba shafaffu da mai ba kawai, da cin moriyar juna irin wanda zai fifita darajar dan Adam da amincewa da bambancin al’umma tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya. Abin burgewa, a wani yanki na jawabin shugaban, ya ce, “A kokarin da ake yi na zamanantarwa, bai kamata a bar wani ko wata kasa a baya ba.”
Bugu da kari, jawabin ya nuna muhimmancin da Sin da Afirka suke da shi a duniya ta fuskar ci gaban zamani, kasancewar kashi daya bisa uku na daukacin mutanen duniya a kasar Sin da Afirka suke rayuwa, don haka ya ce ba za a samu nasarar zamanantar da duniya ba tare da zamanantar da Sin da Afirka ba.
Ina da yakinin cewa shugabanninmu na Afirka sun sake samun wani kwarin gwiwa na kyautatuwar al’amura da ci gaban kasashensu ba tare da hantara ba, a yayin da Shugaba Xi ya furta cewa, ya kamata a hade Sinawa da Afirkawa fiye da biliyan biyu da miliyan dari takwas a karkashin inuwa daya a matsayin wata kakkarfar runduna da za ta fuskanci samar da ci gaban zamani da ya dace da juna, inda hakan “zai rubuta sabon kyakkyawan babi na ci gaba a tarihin bil’adama”.
Irin wannan kawance ne nahiyar Afirka da ake wa kallon koma-baya ta fuskar ci gaba a duniya ta fi bukata, kuma kasar Sin ta nuna sahihancin kawancenta da yankin a zahiri bisa yadda aka samu ci gaba a fannonin sufuri, aikin gona, makamashi da sauran sassan da ta zuba jari na fiye da dala biliyan 200 a nahiyar. Duk da wadannan makudan kudade da ta zuba, da alama kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa Afirka ta fuskoki da dama, kamar yadda Shugaba Xi ya ce, Sin a shirye take ta tallafa wa Afirka wajen kara inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin ’yanci ba tare da katsalandan ba, da fifita yankin a kokarin samar da zaman lumana a duniya.
Hakika jawabin Shugaba Xi ya nuna yadda kasar Sin ke son raya zumunci da ’yan uwantaka da Afirka wajen samar da kwararrun ma’aikata, da yaki da fatara da bunkasa samar da ayyukan yi da kyautata jin dadin rayuwar al’umma da inganta tsaro a zamanance ba tare da shiga-sharo-ba-shanu ba irin na kasashen yamma.