A satin daya gabata ne dan wasa Sadio Mane da Leroy Sane suka yi fada a dakin hutun ‘yan wasa, bayan tashi daga Champions League, kamar yadda wasu jaridu suka wallafa.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce ta doke Bayern Munich 3-0 a wasan farko zagayen kuarter finals a gasar zakarun Turai a Etihad kuma ‘yan wasan biyu sun bai wa hammata iska, bayan tashi daga karawar har sai da aka shiga tsakaninsu.
- Nijeriya Ta Sanya Hannu A Yarjejeniyar Amfani Da Fasahar Shuka Itatuwa Da Kasar Netherlands
- Me Ya Sa Karin Kamfanonin Ketare Suka Samu Ra’ayin Bai Daya Kan Zuwa Kasar Sin Don Raya Kansu?
Rahotanni sun bayyana cewa Mane ya naushi Sane tsohon dan kwallon Manchester City a fuska, har lebensa ya dan tsage sai dai ba wannan ne karon farko da aka yi fada tsakanin ‘yan kungiya daya ba, ko dai a wajen atisaye har a filin wasa ko bayan an kammala gasa.
Tuni kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ta dakatar da dan wasa Sadio Mane daga buga mata wasa ranar Asabar din da ta gabata, ta kuma ce za ta hukunta shi bisa abinda ya faru.
-Ga jerin wasu daga fadan da aka yi tsakanin ‘yan kungiya daya:-
Ibrahimobic da Onyewu
Dan wasa Zlatan Ibrahimobic ya yi kaurin suna wajen fada da abokan wasansa, domin ya taba yi wa Rafael ban der Baart barazanar zai karya masa kafa a Ajad ya kuma naushi Jonathan Zebina a fuska a Jubentus.
To sai dai wanda ya fi muni shi ne wanda ya yi a kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, inda ya yi fada da Oguchi Onyewu, wanda ke buga wasa aro a Newcastle United daga kungiyar Italiya.
Batty da Le Saud
Blackburn Robers ta kasa taka rawar gani a Champions League, bayan lashe Premier League a lokacin ta ziyarci Spartak Moscow a wasa na biyar a cikin rukuni, bayan kasa yin nasara a fafatawar biyar.
A Rashan an ci Blackburn 3-0 a wasan ne Dabid Batty da Graeme Le Saud suka dunga dukan juna da kyar aka raba su. Drinkwater da Jota Ba za ka taba cewa ‘yan wasan da suka yi zaman benci za su bai wa hammata iska ba, abin da ya faru tsakanin Drink Water da Jota kenan a wajen atisaye, kwana daya tsakani da Aston Billa ta ci Leicester City 4-0 – ‘yan wasan Leicester da ba su buga karawar ba na atisaye a Bodymoor Hearth – sai cece kuce ya barke tsakanin Drinkwater da Jota, inda ‘yan wasan Ingila suka yi wa kansu gware, sai da aka shiga tsakaninsu.
Lloris da Son Tottenham ta yi nasara a kan kungiyar kwallon Eberton da cin 1-0 a watan Yulin shekara ta 2020, amma batun da ya fi jan hankali bayan hutu shi ne rigima tsakanin Gugo Lloris da Son Heung-min.
Mai tsaron ragar Tottenham ya tuhumi Son da kin dawowa ya tare kwallo, daga baya suka barke da kokawa har sai da Giobani Lo Celso da Harry Winks suka shiga tsakani, da aka tashi daga wasan sun rungumi juna, sannan bayan tashi daga wasan kociyan kungiyar, Jose Mourinho ya ce abin da ya faru abin ban sha’awa ne.
Mitrobic da Kamara
Aleksandar Mitrobic da Aboubakar Kamara sun dambata a tsakaninsu, bayan da Kamara ya karbe kwallo daga hannun dan Serbia suna Fulham ya buga fenariti a karawa da Huddersfield – akuma bi ci ba.
Adebayor da Bendtner
Emmanuel Adebayor shima daya daga ‘yan wasan da ke fada da abokan wasansa ne, sun bai wa hammata iska da Kolo Toure a Manchester City a
lokacin atisaye a 2011 sai dai tun kafin wannan, Adebayo ya yi fada da Nicklas Bendtner a Arsenal a 2008, wanda aka ce ya yi wa dan kasar Denmark gware a wasan da Tottenham ta ci 5-1 a League Cup wasan daf da karshe.
Robben da Ribery
Za’a iya cewa abin mamaki idan aka ce an yi fada tsakanin Arjen Rubben da Frank Ribery a lokacin gasar zakarun turai na Champions League
tsakanin Bayern Munich da Real Madrid. ‘Yan wasan guda biyu sun yi takaddama kan wanda zai yi bugun tazara, an yi zargin Ribery ya naushi Robben, amma Bayern ba ta ce komai kan lamarin kuma har yanzu babu wata magana daga kungiyar.
Shearer da Gillespie
An yi wani kazamin rikici tsakanin Alan Shearer wanda ta kai sai da aka dangana da Keith Gillespie zuwa asibiti ‘yan wasan Newcastle United a kakar wasa ta shekarar 1997.
Lehmann da Amoroso
Daman dai an bayyana cewa Jens Lehmann ba shi da hakuri ko kadan, ya kuma kalubalanci Marcio Amoroso, bayan da kungiyar Schalke ta zura kwallo a kungiyar su Borussia Dortmund a 2003.
An bai wa mai tsaron raga Lehman jan kati a karawar, wanda ya zama mai tsaron raga na farko a Bundesliga mai wannan tarihin da aka kora karo na hudu – daga baya aka soke kwallon da cewar akwai satar gida – inda suka tashi canjaras.
Ljungberg da Mellberg Mare-mare aka yi tsakanin Freddie Ljungberg da Olof Mellberg, wanda hakan ya ja hankalin manema labarai a lokacin da ake shirin zuwa gasar kofin duniya a kasashen Korea da Japan a 2002.
Ricksen da Radimob
Rahotanni sun bayyana cewa Fernando Ricksen mafadaci ne, wanda ya yi rigima da kyaftin, Bladislab wata daya da komawarsa Zenit sai dai tun kafin nan ya yi rigima da Malaga a lokacin atisaye.
Za’a iya cewa fadan da aka yi tsakanin ‘yan kungiya daya a tarihi yana da yawa da aka yi a baya, za kuma a ci gaba da yi duk da matakan ladabtarwa da kungiyoyi ke dauka a kan ‘yan wasan.