Biyo bayan rokon da aka yi ta yi na samar da tallafi kashi 50 cikin 100 ga gonaki a Jihar Oyo, domin kara samar da wadataccen abinci a jihar, Gwamnatin Jihar ta fara horar da malaman aikin gona da sauran daraktoci a fannin noma a daukacin kananan hukumomin da ke cikin fadin jihar.
Kwamishinan Ma’aikatar Aikin Noma da Bunkasa Noma na jihar, Barista Olasunkanmi Olaleye ne ya bude taron bayar da horon da ya gudana a Sakatariyar Agodi da ke jihar.
- Daminar Bana: Manoma Su Guji Shuka Da Wuri, Su Rungumi Inshora – Masu Ruwa Da Tsaki
- Gwamnatin Tarayya Ta Umarci A Sayar Da Kamfanonin Samar Da Wuta 4
Olasunkanmi Olaleye ya bayyana cewa, an tsara bayar da horon ne ta hanyar yin hadaka da kungiyar ‘Hello Tractor’.
Ya kara da cewa, horon zai taimaka wa wadanda za su amfana; don yin amfani da rajistar daukar bayanan manoman jihar da suka fito daga kananan hukumomin jihar, inda gonakinsu suka kasance.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, bayanan da za a dauka na manoman za su taimaka wa gwamnatin jihar, sanin adadin manoman da ke fadin jihar.
Kazalika, Olasunkanmi ya bayyana cewa, bayanan manoman za su taimaka wajen sanin yawan kadadar noma da manoman za su iya nomawa, nau’in amfanin gona da suke son nomawa, girman gonakinsu, wanda hakan zai bai wa gwamnatin jihar damar sanin irin nau’in tallafin da za ta ba su.
Har ila yau ya sanar da cewa, gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen tabbatar da karfafa gwiwar manoman jihar ta hanyar ba su goyon bayan da ya dace, don rage musu radadin da suke fuskanta, inda ya jaddada cewa; babu shakka yin wannan zai taimaka wajen bayar da damar kara habaka samar da wadattacen abinci a fadin jihar.