Kamfanin rarraba Wutar Lantarki da ke Jos (JED) ya ce kwastomominsa a jihohin Filato, Bauchi da Gombe za su fuskanci matsalar wutar lantarki daga ranar 28 ga watan Agusta zuwa 2 ga watan Satumba.
Kamfanin ya ce, karancin wutar zai fara ne daga karfe 9 na safe zuwa 5 na yamma.
A cikin wata sanarwa da shugaban kamfanin, Dakta Friday Iliya, ya fitar a ranar Asabar a Jos, ya bayyana cewa, kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa TCN ne ya nemi a dakatar da wutar don baiwa injiniyoyi damar sake inganta wutar kamfanin ta hanyar dasa wasu sabbin kayan aiki.
Amma za a cigaba da samun wuta ta hanyar babban layin wutar lantarki (330kv) da ya taso daga Kaduna zuwa Jos.
Don haka sanarwar ta yi kira ga kwastomomin kamfanin da su yi hakuri su jure halin da za a shiga, tare da jaddada cewa kamfanin ya kuduri aniyar inganta ayyukansa don jin dadin kwastomominsa.