Daga Abubakar Abba
Hukumar Kididdiga ta Kasa ta sanya Jihar Legas a zaman daya daga cikin jihohi a kasar nan da ake bin dinbin bashin cikin gida da kuma na kasashen waje, inda aka kiyasta bashin da ake bin ta kasar wajen, ya kai yawan Dalar Amurka Biliyan 15.05 a ranar talatin na watan Yunin
shekarar 2017.
A cewar Hukumar, sauran jihohin dake da mafi yawan bashin kasahen waje sune, Kaduna da Edo da Koros Riba da Ogun.
ta bayyana cewa, jimlar bashin kudaden na cikin gida na jihohin talatin da shida har da Birnin Tarayyar Abuja, ya kai har Naira Tiriliyan N14.06 a watan na Yuni.
A rahoton da Hukumar ta fitar akan basussukan da ake bin jihohin a cikin gida da waje daga ranar talatin ga watan Yuni na shekarar 2017,ya nuna cewa jimlar basussukan na jihohin talatin da shida har da Abuja, ya kai Naira Tiriliyan N14.06.
A bisa kar kasa jimlar bashin, ya nuna cewar jihar Legas ce ke kan gaba na bashin kasar waje da ake bin ta da ya kai jimlar Biliyan 1.3 da kuma bashin kimanin Biliyan 136 na kasar waje, inda jimlar su suka kama, bashin kasar waje dana cikin gida ya zama Dalar Amurka Biliyan 1.45 daga watan Yuni na shekarar 2017.
Sai kuma jihar Kaduna dake bi mata da It bashin Dalar Amurka Miliyan 232, sai jihar Edo nada Dalar Amurka Miliyan 213.95 na kasar waje da ake bin ta.
Rahoton ya ci gaba da cewa, basussukan da ake bin jihohin har da gwamnatin tarayya daga ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2017,yayi dai-dai da bashin da ake bin kasar na kasar waje da kuma na cikin gida da ya kai Dalar Amurka Biliyan 15.05 da kuma Naira Tiriliyan 14.06.
Sai kuma mai bi mata jihar Kaduna da ake bi bashin Dalar Amurka Miliyan 232 jihar Edo kuma ana binta bashin kasar waje na Dalar Amurka miliyan 213.95.
Rahoton ya ci gaba da cewa, basussukan da ake bin jihohin da kuma gwamnatin tarayya na kasar waje da cikin gida ya kai Dalar Amurka Biliyan 15.05 da kuma na Naira Tiriliyan 14.06.
Jimlar bashin da ake bin gwamnatin tarayya na kasar waje, ya kai kashi saba’in da hudu, inda kuma na jihohi tare da Abuja ya kai kashi 26%.
Haka kuma, jimlar bashin da ake bin gwamnatin tarayya na kasar waje, ya kai kashi 78.66 bisa dari, inda jimlar bashin ya rubanya na cikin gida.
Cibiyar ta ce, Jihohi har da Birnin Tarayyar Abuja ya kai kashi 21.34 bisa dari. A bisa kar kasa bashin na gwamnatin tarayya, ya nun cewar bashin cikin gida da ake bin gwamnati ya kai Naira Tiriliyan 7.56.
Jihar Legas ce keda yawan bashi na kasae waje daga cikin jihohi talatin da shida har da Birnin Tarayyar Abuja, inda ya kai kasha talatn da uku bisa dari sai jihar tana da kashi shida bisa dari, inda kuma jihar Edo keda kashi hudu. Kuros Riba nada kashi hudu jihar Ogun nada kashi uku.
Har ila yau, jihar Legas ita ce kan gaba wajen yawan bashi na cikin gida da ake binta a cikin jihohi talatn da shida har da Abuja da kai kashi 10.39, inda jihar Delta, keda kashi 8.04 bisa dari, jihar Akwa Ibom nada kashi 5.18 bisa dari, Abuja kuma nada kashi 5.09 bisa dari, jihar Osun nada kashi 4.90 bisa dari.
Jihar Kuros Riba da jihar Ogun su na da cikin jihohin da ake bin su dimbin a kasar waje, da ya kai Dalar Amurka Miliyan 128.5 da kuma na Dalar Amurka Miliyan 101.2.
Jihar Taraba bashin da ake bin ta na kar waje ya kai Dalar Amurka Miliyan 22.39, Jihar Yobe Dalar Amurka Miliyan 29, inda Jihar Filato ake bin ta bashin Dalar Amurka Miliyan 29.7.
Rahoton yace, ana bin gwamnatin tarayya bashin Dalar Amurka Biliyan 11.1 daga ranar talatin ga watan Yuni na shekarar 2017.