Wani Jirgin saman fasinja na ƙasar Singapore ya yi hatsari mai ban mamaki, domin jirgin ya gamu da gargada ne mai tsanani a sararin samaniya wacce ta zamo kamar kwazazzabo a titin mota, sakamakon hakan yayi sanadiyyar shekawar mutum guda lahira da jikkata wasu talatin (30).
Shi dai wannan jirgi ƙirar Boeing 777-300ER yana kan hanyarsa ne daga Singapore da nufin isa birnin London amma sakamakon wannan mummunar gargada ta sa aka karkata akalarsa zuwa Bangkok, inda ya sauƙa a can.
- Sojojin Iran Za Su Fara Binciken Musababbin Hatsarin Jirgin Da Ya Kashe Raisi
- An Fara Shirin Jana’izar Marigayi Raisi A Iran
Cikin wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar, ya bayyana adadin mutane 211 da suke ciki jirgin mai lamba SQ 321 da kuma ma’aikatansa 18.
Yanzu haka dai ana ci gaba da kula da wadanda suka ji rauni bisa taimakon hukumomin kasar Thailand, kuma tuni an tashi wata tawaga ta musamman ta ma’aikatan lafiya daga Singapore domin ishe su a can.
Dama jirgin sama kan gamu da gargada a sama kamar yadda mota ka iya gamuwa da ita a titi, amma ba kasafai aka cika samun mai tsanani irin wannan ba, Har ya zuwa yanzu ba a san takamaimai abin da ya faru a cikin jirgin ba bayan da ya gamu da gargadar a sama.
Wani lokaci akan iya hasashen gargadar – kuma matuka jirgin sama sukan aika da sako ga takwarorinsu da ke hanya domin gargaɗinsu, to amma kuma matsalar kan faru kwatsam – kuma za ta iya faruwa a ko’ina kuma a kodayaushe.