Daga Sulaiman Ibrahim
Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta ce rahoton leken asirin da ta tattara ya nuna cewa jirgin Alpha Jet (NAF475) da sadarwarshi ta katse daga na’u’rar radar tare da matukansa biyu a ranar Laraba 31 ga Maris, 2021 na iya yiwuwa hadari yayi.
NAF, ta ce har yanzu ba a san musabbabin hatsarin ba da kuma inda matukan jirgin biyu suke.
Matukan jirgin su ne Laftanar John Abolarinwa da Laftanar Ebiakpo Chapele.
Wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a da Labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Juma’a wacce LEADERSHIP ta samu, ta ce har yanzu ana ci gaba da bincike don kubutar da jirgin da matukansa ta hanyar amfani da jirgin saman NAF da kuma Dakarun Musamman na NAF da sojojin Nijeriya na kasa.
” ya zuwa yanzun, NAF ba ta yanke takamaiman abinda ya faru da jirgin ba, Amma duk da haka muna da kwarin gwiwa cewa nan ba da jimawa ba za a gano jirgin tare da kubutar da matukansa. “in ji Gabkwet.