Abba Ibrahim Wada" />

Juventus Ta Yi Fatali Da Tayin Madrid A Kan Dybala

Rahotanni daga kasar italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dake kasar  tayi fatali da tayin kudi fam miliyan 170 tare da karbar dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Carlos Vasquez domin ta ba da dan wasanta, Paulo Dybala.

A kwanakin baya ne dai aka bayyana kungiyar Real Madrid  a matsayin kungiyar da take zawarcin dan wasan dan asalin kasar Argentina wanda a yanzu yake bugawa Jubentus din wasa.

Dybala, mai shekaru 25 a duniya yaja hankalin manyan kungiyoyi a duniya irinsu Barcelona, da Manchester United da Manchester City inda kungiyoyin suka shirya tsaf domin taya dan wasan.

Sai dai a cikin wannan satin ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid  ta taya dan wasan fam miliyan 70 sannan kuma da alkawarin cewa idan har Juventus din ta yarda zata bata dan wasa Baskuez duk acikin cinikin na Dybala.

Real Madrid dai tana zawarcin Dybala ne wanda take ganin zai maye mata gurbin Cristiano Ronaldo wanda yabar kungiyar a watan daya gabata zuwa Juventus din akan kudi fam miliyan 105

Kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dai ta bayyana cewa tana bukatar kudi kusan fam miliyan 200 kafin ta saki dan wasan nata Dybala wanda ta siyo daga kungiyar Palarmo shekaru hudu da suka gabata.

Real Madrid  dai tana neman dan wasan gaba mai zura kwallo a raga inda a kwanakin baya ta nemi dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard sai dai watakila kungiyar za ta hakura da dan wasan idan har tasamu Dybala.

Exit mobile version