Tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya gargaɗi ‘ƴan Nijeriya da ka da su kuskura su zaɓi masu kashe mutane a zaɓe mai tafe.
BBC ta rawaito cewa, Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a garin Uyo na Jihar Akwa Ibom a taron addu’o’i da aka yi kan cikar jihar ta Akwa Ibom shekara 35 da samun jiha.
- Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Gana Da IBB Da Abdusalamu A Minna
- Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Gana Da IBB Da Abdusalamu A Minna
“A shekarar 2023, kada ku yi kuskuren zaɓen masu kashe mutane,” in ji Jonathan. Waɗanda za su ɗauki wuƙaƙe da bindigogi da duk sauran makamai su je su kashe mutane saboda siyasa maƙiyan al’umma ne. Idan ka kashe wani domin ka zama shugaba, za ka ci gaba da kashewa domin ka kasance shugaba,” kamar yadda Mista Jonathan ya bayyana.
Haka kuma Mista Jonathan ɗin ya yaba wa Gwamnan Udom Emmanuel na jihar kan ayyukan ci gaba da ya kai jihar.