Jam’iyyar APC ta shawarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da ya sa lauyoyinsa su daukaka kara a gaban kotu maimakon gudanar da zanga-zanga a titunan kasar nan.
Mista Bayo Onanuga, Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ne, ya bayar da shawarar a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
- Jam’iyyar NNPP Ta Bukaci Jami’an Tsaro Su Tabbatar An Yi Sahihin Zabe A Kano
- Kotun Koli Ta Tabbatar Lawal Dare A Matsayin Dan Takarar Gwamnan PDP A Zamfara
Bayanin hakan dai shi ne martanin jam’iyyar APC ta fitar kan zanga-zangar da ‘yan jam’iyyar PDP suka shirya a karkashin Atiku na nuna adawa da sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Onanuga ya kuma shawarci Atiku da ya mutunta shekarunsa da kuma babban ofishin mataimakin shugaban kasar Nijeriya da ya taba yi.
“Lokacin da Atiku Abubakar da ya sha kaye ya shaida wa duniya a makon da ya gabata cewa zai nemi hakkinsa a kotu kan sakamakon zabe, don haka ko kadan ba mu san cewa zai tafi kotu ba.
“Bisa ga magabata na siyasa, ba abin mamaki ba ne, cewa Atiku, kwanaki bayan haka, ya jagoranci gungun masu zanga-zanga, a Abuja zuwa hedikwatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
“Abin da Alhaji Atiku da jama’arsa suka nuna a yau wani sabon salo ne daga wanda ya sha kaye a zabe.
“A yayin da Atiku ya shirya wasan kwaikwayo na banza, mun kasa ganin yadda tattakin da jama’a da dama suka yi zuwa INEC zai samar da duk wata nasarar da ya samu a gare shi da ‘yan jam’iyyarsa ta PDP,” in ji Onanuga.
Atiku dai da jiga-jigan jam’iyyar PDP sun yi zanga-zangar nuna adawa da sakamakon zaben da INEC ta ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasar Nijeriya.