Connect with us

LABARAI

Ka Iya Bakinka Kan Ango Abdullahi – Kashedin AYCF Ga Adesina

Published

on

An ja kunnen Kakakin Shugaban Nijeriya, Mista Femi Adesina, da ya iya bakinsa kan dattawan Arewa, musamman Farfesa Ango Abdullahi, bisa amfani da kalaman cin zarafi a kansu.

Kashedin hakan ya fito ne daga bakin kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultatibe Forum – AYCF) cikin wata sanarwa da su ka raba wa manema labarai jiya Talata, ciki har da LEADERSHIP A YAU.

A ranar Litinin ne dai Mista Adesina ya bayar da wata sanarwar da ta yi martani kan sanarwar da kungiyar Dattawan Arewa a karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi, wacce ta soki lamirin Gwamnatin Tarayya kan batun tabarbarewar tsaro a yankin Arewacin Nijeriya.

Sanarwar AYFC mai dauke da sa hannun shugabanta kasa, Alhaji Yerima Shettima, ta ce, “hankalinmu ya kai kan yadda mai magana da yawun Shugaba Buhari, Femi Adesina, ya yi amfani da lafazi na cin zarafi a kan dattijonmu da a ke matukar girmamawa – Farfesa Ango Abdullahi, saboda kurum ya bayyana gaskiyar abinda ke damun miliyoyin ’yan Arewa.”

AYCF ta kuma ce, “Femi Adesina ya ci mutuncin Arewa kuma mun damu da irin kalmomin da ya yi amfani da su, wadanda mun yi imanin cewa, ba zai yi amfani da su ba a kan dattawan yankin Yarabawa bisa kowacce irin hujja. Don haka mu na bukatar ya janye munanan kalmomin da ya yi amfani da su a kan Farfesa Ango Abdullahi da sauran dattawan kungiyar Dattawan Arewa (NEF).

“Ba mu ga ta inda fadin gaskiya da Farfesa Ango Abdullahi ya yi ba kan kashe-kashen da a ke yi a Arewa zai bayar da damar da Femi Adesina zai yi amfani da munanan kalamai a kan dattawanmu ba.

“Mu na kallon lamarin a matsayin abin kunya a ce Kakakin Shugaban Kasa ba shi da balagar zance wajen fakewa da guzuma kan fuskantar zahirin gaskiya kan halin da Nijeriya ke ciki a yau, inda kuma lamarin ya fi baci a Arewa.

“Mu na masu fayyace cewa, ba za mu sake yarda da yin amfanin cin zarafi kam dattawanmu ba, domin wannan ba shi ne karo na farko da Mista Adesina ya ke amfani da kalaman cin zarafi a kan dattawan yankinmu ba, amma dai mu na fata wannan ya zamo karo na karshe.

“Mu na kuma masu sanar da Adesina cewa, kowa da ya iya bakar magana. Don haka tilas ne a tsayar da cin zarafin Arewa nan take.”

A karshe sanarwar ta karkare da kira ga dukkan ’yan Arewa da su yi watsi da irin wadannan kalaman batancin da kungiyar ke zargin Adesina da yi kan dattawan yankin, musamman ga Farfesa Ango da kungiyar ta NEF.

“Tura ta kai bangi fa!” in ji Shettima, shugaban kungiyar ta matasan Arewan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: