Aure a kabilar Bayankole na da matukar muhimmanci duba ga yadda iyaye ke samo farin ciki da alfahari daga auren ‘ya’yansu.
Wannan kabila da ke kasar Uganda, tana da al’ada mai ban mamaki game da abin da ya shafi aure. idan mace ta cika Shekaru takwas zuwa tara, wajibi ne Innarta ta koyar da ita yadda ake zaman aure a kabilar Bayankole.
- Abubuwa Uku Da Za A Yi Farashin Kaya Ya Sauka A Nijeriya – Dakta Saleh
- Mai Dakin Shugaba Xi Jinping Ta Sha Shayi Tare Da Mai Dakin Shugaban Kasar Hungary
Budurci a bisa al’adar Bayankole, abu ne da ake lura da shi sosai saboda guje wa jima’i kafin aure.
Kabilar Bayankole na la’akari da siririn jiki domin kiyaye gina jiki mara jawo hankali. A ganin su, kiba ta fi ban sha’awa da jawo hankalin samari wajen zaben mata a kan siririn jiki. Haka, idan mace ta cika shekaru takwas zuwa tara, ana bukatar ta fara amfani da abubuwan da ke gina jikin Dan’adam. Ana haka ne saboda a gaggauta samun nauyi da Kiba ga ‘ya mace domin samun mijin aure.
Aure a kabilar Bayankole ya kunshi bukukkuwan da shagulgula da dama ciki har da lokutan kyauta wato “kuhingira” inda dangi da kawayen amarya ke kawo mata kyaututtuka kamar shanu da sauran kayan abinci wanda za ta kai gidan aure.A ranar daurin aure kuwa, ana shirya liyafa a gidan amarya inda mahaifinta ke yanka bijimin sa, yayin da su ma gidan ango ke shirya liyafa ta kasaita domin kawata auren.
Amma da farko kafin a kai ga daura aure, akwai al’adar biki da ake muhimmantawa sosai wadda ta kunshi gwaje-gwaje da Innar amarya ke gudanarwa. Al’adar ta kunshi Innar amarya ta gwada karfin jima’in ango ta hanyar saduwa da shi domin tabbatar da shin yana da karfin jima’in gamsar da ‘yarsu ko a’a.
Lokacin da suke jima’i, Innar za ta rika lura da kuma koyan abubuwan da ango ya fi sha’awa da bukata lokacin kwanciyar aure, domin nuna wa ‘yar da za a aurar abubuwa na gyara zaman aure kamar salo na jima’i da angonta ke so.
Bayan tabbatarwa, Innar za ta koya wa amarya duk wadannan abubuwa da ta gano domin amarya ta tare cikin shiri kai-tsaye a gidan mijinta cikin kwarewa da kuma sa albarka gare ta daga Innar da yi mata wannan gagarumar gudanmawa. Masu Karin magana dai sun ce, Allah Daya Gari Bamban!
Â
Mun yo muku tsaraba daga shafin Klaus Musenge