Jirgin musamman na Ethopia Airline ya tashi daga jihar Kaduna zuwa Adis Ababa da sauran kasashen duniya,don fara jigila daga kasa zuwa kasa.Idan za a iya tunawa dai Ethopia Airline shi kadai ne jirgin da ke zuwa kasashen duniya da ke sauka a filin jirgin saman Nmandi Azikiwe da ke Kaduna lokacin da aka kwashe tsawon mako shida ana gyaran filin.
A lokacin da yake jawabi wajen bikin tashin jirginna farko, bayan kammala aikin filin jirgin karamin ministan kula da filayen jiragen sama Sanata Hadi Sirika, ya tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na bayar da cikakken goyon baya a harkar sifirin jiragen sama. Saboda haka, sai ya yi kira ga sauran kamfanoni jiragen sama na kasashen Afirka da su kulla dangantaka da filin jirgin na Kaduna.
Shi ma da yake nasa jawabin shugaban Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, InjiniyaSaleh Dunoma, ya bayyana cewa, sauka da tashin jiragen sama abu ne mai matukar muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, saboda haka, al’ummar jihar Kaduna za su amfana da wannan filin jirgin sama matuka, sannan su ma Hukumarsu za ta samu kudaden shiga wanda za su taimaka mata wajen ci gaba dakula da filin jirgin.
Injiniya saleh ya ci gaba da cewa, fara jigilar zuwa kasashen duniya da jirgin Ethopia Airline ya yi kamar wani mabudi ga nsauran kamfanonin jiragen sama na duniya, domin yawan fasinjoji zai karu, wanda kuma zai sa sauran kamfanonin jiragen sama na duniya, su shigo a dama da su.Saboda haka, ya ce, za su bayar da cikakken goyon baya ga dukkan kamfanin da ya zo na ganin ya samu nasara.