Wata motar Siyana ta haya ce cike da fasinjoji daga Kano zuwa Abuja, ga dukkan alamu motar na dauke ne da masu zazzafan babbance-banbancen ra’ayoyi a bangaren da ya shafi rayuwa. Kusan duk cikin awa guda a kan tafka mahawara ta tsawon mintina arba’in a cikin motar.
Ashe wancan kace-nace da ake ta faman yi cikin motar babu kakkautawa, na matukar sosa ran wani Farfesa da ke cikin fasinjojin, wanda ya samu kansa cikin motar bisa lalura, motarsa ce ta samu matsala a garin Kaduna, duba da tsabar muhimmancin da tafiyar tasa ke da shi, hakan ya tilasta masa shiga motar hayar. Can dai ana tsaka da tafiyar ne, Farfesa ya rika nunawa sauran fasinjojin da ke wannan mahawara da taki-ci taki-cinyewa cewa, sakamakon katutu da jahilci ya yi musu ne yasa suke tafka irin wannan mahawara ta jahilci maras muhimmanci da ma’ana.
Cikin motar, ashe wani tuni ya kule da irin yadda Farfesa ke bayani gatsa-gatsa ga mutane ba tare da wani martaba su ba. Mutumin ya yi kokarin kwabar Farfesa cikin cewa; “Allah Shi gafarta Malam, duk da ban san ko kai wane ne ba, amma dai zai yi kyau a rika tausasa harshe idan aka tasamma kawo wani gyara. Nan take fuskar Farfesa ta canza damkar an yi masa tsabga, ya amsa cikin fushi da cewa;
“Ka san kuwa ko ni waye kake da’awar son cin gyara na? Yau kimanin shekara ta goma da zama cikakken Farfesa, idan ban da ma kaddara mene ne zai shigo da ni cikin wannan kwarababbiyar mota kucaka! Kawai na shigo ne bisa kaddarar lalacewar da motata ta yi a hanya ne. Uwa-uba, idan ban da cewa yau da yamma zan gana da Mataimakin Shugaban Kasa, da sai na tsaya har an kammala gyaran sannan na tawo. Saboda kun ga mutane a arha tare da ku cikin motar haya, shi yasa kuke fuskantar su da shirme da jahilci, mtsm!.
Bayan mintina hamsin ana cikin kwada gudu ne kwatsam ‘yan fashi suka tare motar. Su kimanin talatin ne, ba tare da wani bata lokaci ba suka yi wa motar kawanya. Ga hannayensu rike da irin manyan bindigogin nan da ake yi wa lakabi da AK 47, suna fadin, “Ku fito ku fito shegu barayin gwamnati!”.
Bayan an umarci duk wanda ke cikin motar cewa ya fito ya hau layi, daga nan sai Ogan ‘yan fashin wani dogo murdadde baki wuluk tamkar zunubi, ya rika kallon wadannan fasinjoji daya bayan daya, idon nan jajazur, ya ci-gaba da fadin;
“Shegu barayin boye, yawancinku da ke kai-gwauro su kai-mari bisa wannan hanya, ko dai manyan ma’aikatan gwamnati ko kuma ‘yan korensu, shegu barayi masu lasisi. Ku sani ai da ma an ce dare dubu na barawo, amma guda daya tak na mai kaya ne”.
Sai jagoran ‘yan fashin ya biyo layi yana tambayar sana’ar fasinjojin daya bayan daya. Wani ya ce dako yake yi a Kasuwar Kurmi, wani tallan Turmi a Kasuwar Barci da ke Kaduna, wani ya ce yana sanaAar Shushaina a Yanya da ke Abuja, haka-haka dai kowa ya rika jingina da karamar sana’a don ya samu a tausaya masa. Ko da Ogan ‘yan fashin ya yi arba da Farfesa, sai ya ce da shi;
“Kai fa! Wannan mai gashin bakin, mece ce taka sana’ar? Nan take Farfesa ya amsa da cewa, “Yallabai ni Dan-gambara ne”. Jin Farfesa ya kira kansa da Dan-gambara, sai wani cikin ‘yan fashin ya ce; “Maigida me zai hana wannan Dan-gambara ya dan rera maka wata waka tun da ai yau ne kewayowar ranar haihuwarka”.
Ko da aka nemi Farfesa da ya fito ya dan rera wa Oga waka, sai ko ya fito yana gaggatsa baitoci kaca-kaca yana rangaji gami da lumshe idanu. Shi kansa da za a ce ya baiwa kansa maki, ko shakka babu ka da kansa zai yi. Ashe cikin tawagar ‘yan fashin, akwai wani da gambarar ma gadon gidansu ce. Saboda haka, ganin irin yadda Farfesan ke neman tozartar musu da gadon gida, sai ya nemi Ogan nasu da ya yi masa alfarma ya damka masa Farfesa a hannunsa ko da na tsawon Wata guda ne, don ya gogar da shi a harkar gambarar.
Gabanin jin amsar da Ogan zai ba da, nan da nan sai ga Farfesa ya zube gaban jagoran fashin yana ta gabza kuka gami da yi masa magiyar cewa don Allah ya yi masa rai, ya kuma yi wa gyatumarsa rai kada a damka shi hannun wancan mutumi. Ya ci-gaba da cewa; “Wallahi yallabai matana uku da ‘ya’ya ashirin da biyar. Sannan yallabai, da uwata da ubana duka an kwantar da su jiya a Asibitin Zana na Kano. Ni ne cinsu, ni ne shansu. Idan suka ji kun rike ni, Wallahi Allah za su iya hadiyar zuciya su mutu. Yallabai idan ma ban iya gambara ba, ai da ma babana ya yi wannan tunani, shi yasa ma ya hada ni da wanda zai koya min rawar koroso, ya ce mai yiwa a koroson ne abincina yake ba a gambara ba. Don Allah yallabai a yi min rai ka da a ba shi ni”. Jin kalaman Farfesa, sai Ogan ‘yan fashin ya sheke da dariya, kana ya ce, “Ashe dai ana tsoron iya in ji ‘ya’yan Mayya”.
Sai Farfesa ya yi tsaki, kana ya ce; “Amma dai kai jahili ne! ba ka san ilmi kogi ne ba? Ai hatta wannan abin da ka ga na yi, akwai shi a farfajiyar ilmi”. Nan take kowa a cikin motar ya kece da dariya. Aka hau sowa ana fadin; “Farfesa! Farfesa!! Farfesa!!!”.