Wani babban jami’in Ƴansanda, ASP Shafi’u Bawa, na rundunar 61 Police Mobile Force (PMF), an tsinci gawarsa a dakinsa a garin Kontagora, Jihar Neja, a ranar Asabar, bayan da ake zargin ya kashe kansa.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gano gawar ASP Bawa rataye a saman silin ɗin ɗakinsa. Mahaifinsa, Malam Usman Bawa, ne ya fara gano lamarin kafin ya kai rahoto ofishin ‘yansanda na Kontagora.
- Matsalar ‘Yan sandan Amurka Ta Nuna Karfin Tuwo Na Kara Tsananta
- Abin Fashewa Ya Hallaka Mutum Guda, Ya Jikkata 6 A Neja
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa: “A ranar 8/2/2025 da misalin ƙarfe 2 na rana, an samu rahoton cewa ASP Shafi’u Bawa na 61 PMF Kontagora ya kashe kansa ta hanyar rataya, ba tare da sanin dalilin da ya kai shi hakan ba.”
Ya ƙara da cewa an ɗauki gawarsa, aka miƙa wa iyalansa domin binne shi, sannan bincike ana ci gaba da bincike don gano musabbabin lamarin.