Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Tajudeen Abbas, ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya rufe idonsa ya dauki kwararan matakai kan mukarrabansa da suka kasa gudanar da ayyukan da ke wuyayensu.
Ya ce, ta hanyar fitar da wadanda suka kasa kokari daga cikin hadiman shugaban kasa za a samu natija a yaki da ake yi kan matsalolin tsaro a fadin kasar nan.
- Bikin Al’adun Gargajiya Na Rigata Karo na 3 Zai Gudana A 8 Ga Fabrairu A Yauri
- Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Kai Don Ciyar Da Jihar Gaba
Ya kuma ba da shawarar cewa a bullo da wasu sabbin dabarun hikima wajen tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan ta Nijeriya.
Abbas ya yi wannan kiran ne a ranar Talata yayin da majalisar ta dawo hutun da ta tafi na bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara.
Da yake kokawa kan karuwar matsalolin tsaro a Nijeriya wanda har kana samu salwantuwan rayukan ‘yan Nijeriya da daman gaske a ‘yan kwanakin baya a jihohin Filato, Kaduna da wasu sassan kasar, Abbas ya lura kan cewa, muddin ba a tashi tsaye aka kawo karshen matsalolin ba, nan gaba matsalar tsaro zai zama babban barazana ga daurewar kwanciyar hankalin kasar.
Ya ce, “Duk da daukan matakan tsaro daban-daban, amma har yanzu kalubalen matsalar tsaro na ci gaba da addabar jama’a, muna sako-sako da kokarinmu da matakin da muke dauka na shawo kan matsalolin da ke barazana ga daurewar zaman lafiya da kwanciyar hankali hadi da ci gaban kasarmu.
“Akwai bukatar mu tunatar da kanmu cewa dabarun tsaro da ake bi na tsawon lokaci ba su wadatar da mu ba. Don haka, lokaci ya yi da za a zauna a sake tunani a fito da wasu muhimman dabarbarun da za a dauka da kuma tsare-tsaren da za su taimaka wajen kawo karshen matsalolin tsaro da suke addabarmu.
“Ga kuma jaruman jami’anmu na tsaro, a yayin da muke jinjina wa kokarinku da sadaukarwarku, lokaci ya yi kuma da za ku sake waiwayar hanyoyi da dabarbarun da kuke bi domin ingantasu da sabuntasu. Makiya na sauya taku, dole ne muma mu yi hakan. Na kalubalanceku a kan wannan da cewar ku tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kawukanku na kare mana jama’a da dukiyarsu.”
Ya ce, a matsayinsa na dan kasa da ya damu kuma lamarin ya shafa, matsalar tsaro ya dameshi kuma na daga cikin abubuwan da suka tsaya masa a wuya da sauran al’umman kasa.