Kalaman El-Rufai Bai Da Ce Da Musulmi Na Kwarai Ba -Majalisar Limamai

An bayyana zafafan kalaman Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ga abokan hamayyar siyasarsa a matsayin furucin da bai da ce a jishi daga bakin cikakken Musulmi mai ikirarin yana da imani ba.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Majalisar Limamai da Malamai na Jihar kaduna, Sheikh Usman Abubakar Baban Tune, a yayin da majalisar ta kira wani taron gaggawa na manema labarai a Sakatariyar kungiyar dake kaduna.

Majalisar Limamai da Malaman, tayi Allah waddai da irin salon siyasar wasu manyan daga cikin masu fada a ji a wannan jihar, musamman irin yadda suke fitowa bainar jama’a, suna furta wasu furucin munanan kalamai akan Abokan hamayyar siyasarsu wanda duk mutum mai amsa sunansa musulmi kuma mumini ba zai aikata hakan ba.

“Wannan Majalisa ta abubuwan takaici wadanda wasu batagarin ‘yan siyasa suke aikatawa, abubuwan da suna iya zama hadari ga Al’ummar wannan jiha tamu ta kaduna, da ma Nijeriya baki daya. Domin mun lura akwai wasu miyagun ‘yan siyasa wadanda siyasarsu ita ce siyasar banga, suna siyasa suna yin barna da ta’adanci, ko dai a wajen taruka, ko a wajen zabe, ko a makamantan wadannan wurare. Domin suna iya sanya ‘yan ta’adda su yi sare-sare, da yima jama’a raunuka, da kisa, da kone konen dukiyoyi, da sauran barnace barnace, da kuma sauran miyagun ayyuka na ta’addanci, amma duka suna yin wadannan miyagun ayyuka ne na barna da sunan siyasa, ko dimokaradiya.”

Majalisar Limamai da Malaman ta kara da bayyana cewa, “Akwai wasu ‘yan siyasa wadanda siyasa a wajensu ita ce’, batanci, da cin mutunci, da zubar da mutunci da kiran suna, tare da zagi da tsinuwa ga abokan hamayyarsu na siyasa, tare da umurtan mabiyansu da yin ta’addanci a kan abokan hamayyarsu na siyasa, kuma suna yin wannan ne karara a gaban duniya da miliyoyin jama’a, babu kunya babu tsoron Allah, wanda Shari’ar Musulunci ta Haramta yin hakan, kuma tayi ma mai yin hakan tanadi mummunar azaba, kamar yadda Allah ya zo a cikin Hadisin Annabi Muhammadu (S.A.W), inda yake cewa: Mutum baya yin alwashi a kan abin da baya da shi, bai mallake shi ba, kuma zunubin la’anar Musulmi kamar zunubin kashe shi ne.”

Sun kuma kara da bayyana cewa,” Idan Bawa ya tsine ma wani abu! To ita tsinuwar sai ta hau sama, sai ta iske an kulle kofofin sama, sai ta dawo domin ta kutsa karkashin kasa, sai ta cimma an kulle kofofin kasa, sai tayi dama, tayi hagu, idan bata sami wajen shiga ba, to sai ta je ga wanda aka tsine ma wa, idan ta ga ya cancanci tsinuwar, to sai ta fada masa, idan kuma taga bai cancanci tsinuwar ba, to sai ta koma ta afka a kan wanda ya furta ta.”

 

Majalisar Limamai da Malaman ta Jihar kaduna, ta kuma nuna bacin ranta matukar gaske game abin da suka kira siyasar karfa karfa da a ka gudanar a yayin zabukan Kananan Hukumomi da ya gudana a fadin Bihar Kaduna. Inda suka bayyana cewa,” Abin da bincike ya tabbatar, dangane da zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa a wannan jiha tamu, binciken mu ya nuna mafiya yawan jam’iyyun siyasa, sun aikata kama karya ne, da karfa karfa, wajen dora ‘yan takaran da shi jama’a ke so ba, kuma bashi ne maslhar al’umma ba, wanda ita maslaha al’umma shi ne kashin bayan kafa jam’iyyun siyasa. Wanda wannan karfa karfa na iya sanya mafiya yawan wadanda suka aka daura a kujerun shugabancin kananan hukumomi Magi yawancinsu wawaye ne, ko azzalumai, ko kuma wadanda basu da mutunci a cikin al’umma. ”

 

Daga karshe, Majalisar Limamai da Malaman ta na kira ga dukkan Malamai masu tafsir da su ji tsoron Allah, kada su kauce ma ka’idojin tafsir, wannan muna kira ga Al’umma Musulmi da a duba watan Ramadan a ranar duban fari, kuma Idan aka ga watan ayi kokarin sanar da Shugabannin da suka da ce.

 

Sai dai a nasu bangaren Gwamnatin Jihar Kaduna, ta musanta wadannan zargi da Majalisar Limamai da Malamai suka yi akan Gwamnatin Jihar Kaduna. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Babban Darakta mai kula da harkokin Addinai ta Jihar Kadun, Injiniya Muhammad Namadi Musa, wanda ya bayyana cewa wannan zargi bai da tushe balle makama.

Injiniya Namadi Musa ya ce, a iya sanin sa yasan babu inda gwamnati tayi wani karfa karfa wajen daura wani dan takara wanda jama’a basaso. Sannan ya kuma bayyana zargin da ake yi ma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed Elrufai, na cewa ya furta wasu munan kalamai a kan abokan hamayyar siyasarsa da cewa, ajuzanci ne irin na Dan Adam, wanda bai wuce kuskure.

Babban Darktan, ya kuma janyo hankalin Majalisar Limamai da Malaman da cewa, a maimakon fitowa kafafen watsala labarai da suka yi suna sukar wannan Gwamnati, kamata ya yi, su nemi zama a addinance domin bayyana ma gwamnan kuskuren yin haka, da kuma duk wani abu da suke ganin ana yi ba dai dai ba. Domin a cewarsa, Malamai fa sune wanda Allah ya daura ma nauyin yiwa kowane shugaba nasiha, amma ba ruruta wutar fitina ba, ko nuna goyon bayansu ga wani bangare. A cewar Babban Darakta mai kula da harkokin Addinai ta Jihar Kaduna, Injiniya Muhammad Namadi Musa.

Exit mobile version