A kwanan ne ne firaminista Sanae Takaichi ta kasar Japan ta tsaya a gaban kyamarori yayin wani zama a majalisar dokokin kasar, ta furta wasu kalamai na katobara masu ban-takaici, kan cewa, matukar kasar Sin ta dauki matakin soji a kan yankin Taiwan, hakan zai zama barazana ga dorewar kasar ta Japan. Wannan katobara ta watsu tamkar wutar daji a duk fadin yankin Asiya, har ma da sauran sassan kasa da kasa, bisa yadda ta kunshi tsokana da kuma neman tayar da zaune-tsaye a sabon zamani.
Ga wadanda za su iya tunawa da tarihi, sun san ba wannan ne karon farko da Japan ta saba yin kasassaba ba. A cikin manyan kaba’irorin da ta tafka, ta yi amfani da kalmar “kare kai” da “tabbatar da tsaro” wajen kaddamar da munanan farmakin soji. A cikin shekarun 1930 da 1940, shugabannin kasar sun ba da hujjar cin zarafi da aika-aikar da suka tafka a Manchuria ta kasar Sin, da sauran sassan yankin Pacific, a matsayin wai “kokarin kare dorewar kasar Japan”. Ta aikata mummunan zalunci na kisan gilla a Nanjing, da sauran bala’o’in da ta haddasa a yankin Asiya, har dai daga bisani ta ga iyakar kanta a shekarar 1945.
Katobarar Takaichi, duk da cewa ta furta ce a cikin wannan karni na 21, amma tana dauke da sako iri daya da wadda aka taba furtawa a kasar lokacin mulkin danniya. Ta danganta makomar Taiwan kai-tsaye da dorewar kasar Japan, inda hakan ke nuna kasadar da take neman yi a kan sake farfado da tunanin Japan na mamaye makwabtanta maimakon zama tare cikin lumana.
Ganin irin hadarin dake tattare da katobarar Takaichi musamman wajen kawo cikas ga zaman lafiyar da ake ta kokarin karfafawa a yankin Asiya, kasar Sin ba ta bata lokaci ba wajen yin Allah wadai da katobarar tata, tare da mayar da zazzafan martani ta hanyoyin da suka dace a ciki da wajen kasar.
Yanzu haka, Sinawa da dama sun suka soke tafiye-tafiye zuwa Japan baki daya, lamarin da ke kawo cikas ga bunkasar tattalin arzikin kasar ta Japan, kasancewar matakin na Sinawa zai iya haifar wa kasar da asarar adadin da ya kai kudin kasar JYE tiriliyan 2.2, kwatankwacin kudin Sin yuan biliyan 101.6, kamar yadda aka ji daga wani masani a kwalejin bincike ta Nomura Takahide Kiuchi. Kuma wannan fa, baya ga asarar da za ta tafka ce a bangaren cinikayya da kasar Sin, wanda ko a bara, adadin kasuwancin da aka yi a tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 308.3.
Tarihi dai ba ya karya kuma ya kamata ya zama madubi ga firaminista Takaichi wajen yin waiwaye a kan shugabannin da suka gabace ta wadanda suka kai kasar suka baro. Kazalika, matukar kasar na son zama wani sabon karfi mai matukar fada-a-ji a yankin Asiya, ta bi hanyoyin lumana da kyautata mu’amala maimakon fito-na-fito da tayar da fitina.
Hakika dai, kalaman Takaichi na da matukar ban-takaici! (Abdulrazaq Yahuza Jere)














